Home Back

Man United na daf da yin wuf da Nevez, Juventus na shirin ɓata ruwan Arsenal

bbc.com 2024/8/21
.

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta amince da yarjejeniya tsakaninta da dan wasan Crystal Palace Michael Olise, Brighton na shirin sanar da Fabian Hurzeler a matsayin sabon kocinta, Fulham ta ki amincewa da farashin Joao Palhinha na Bayern Munich.

Chelsea ta amince da yarjejeniya kai tsaye tsakaninta da dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 22, kuma tana shirin tattaunawa kan jadawalin biyan kudin da za ta biya domin daukarsa bayan sakinsa daga Crystal Palace. (Givemesport)

Fulham ta sanya farashin dan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, a kan fam miliyan 30 inda ita kuma Bayern Munich ta ki amincewa. Barcelona da Manchester United suma suna zawarcin Palhinha. (Sky Sports)

Manchester United da Tottenham na shirin fafatawa wajen neman dan wasan Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze, mai shekara 25. (Football Insider)

Newcastle ta daina neman kulla yarjejeniya da Valencia kan golan Jojiya Giorgi Mamardashvili, mai shekara 23, bayan da, kungiyar ta ki amincewa da Yuro miliyan 30 duk da cewa kulob din na Sipaniya ya kimanta shi kan Yuro miliyan 35. (Relevo Espanya)

West Ham na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan bayan Argentina Nehuen Perez, mai shekara 23, daga Udinese. (Gianluca Di Marzio)

Brighton na sa ran sanar da Fabian Hurzeler, wanda ya jagoranci St Pauli zuwa gasar Bundesliga a watan da ya gabata, a matsayin sabon kocinta a wannan makon. (Guardian)

Bayern Munich na sha'awar dauko dan wasan bayan Chelsea Levi Colwill, mai shekara 21, inda bayanai ke cewa har an yi wata tattaunawa ta farko don sayen dan wasan na Ingila. (Sky Germany)

Atletico Madrid ta sake farfado da sha'awarta ta neman dan wasan tsakiya na kasar Denmark, mai shekara 28, Pierre-Emile Hojbjerg, bayan da cinikin sayansa a kan fam miliyan 15 daga Tottenham ya lalace a bara. (Mail)

Leicester ta bayyana tsohon kocin Brighton da Chelsea Graham Potter a matsayin wanda zai iya maye gurbin Enzo Maresca amma kuma suna la'akari da sauran wadanda ke zawarci ciki har da Steve Cooper. (Guardian)

Crystal Palace na shirin daukar dan wasan tsakiya na Japan Daichi Kamada a ɓagas (kyauta) bayan dan wasan mai shekaru 27, wanda ya shafe kakar wasa ta bara a Lazio, ya kammala matakin farko na gwajin lafiyarsa. (Fabrizio Romano)

Sporting Lisbon na sha'awar dan wasan Wolves Chiquinho, mai shekara 24, kuma za a shirya biyan kusan Yuro miliyan 10 kan dan wasan na Portugal. (Ya Jogo Portuguese)

Chelsea ta amince da yarjejeniyar kai tsaye tsakaninta da dan wasan bayan Brazil Pedro Lima, mai shekara 17, wanda ya fara taka leda a Sport Recife a watan Janairu. (HITC)

Dan wasan Amurka Brendon Aaronsen, mai shekara 23, wanda ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro a Union Berlin, yana shirin ci gaba da zama a Leeds United duk da cewa yana sha'awar Jamus. (Athletic)

Juventus na shirin tattaunawa da Aston Villa nan da kwanaki masu zuwa kan cinikin dan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 26 wanda Arsenal ta ƙwallafa ranta a kansa, amma cinikin zai iya faruwa ne kawai idan dan wasa ya koma Villa daga kulob din Italiya. (Fabrizio Romano)

Ipswich na shirin karawa da Besiktas ta Turkiyya kan dan wasan Rangers da Wales Tom Lawrence, mai shekara 30. (Mail)

Manchester United ta samu kwarin guiwa kan zawarcin dan wasan Benfica da Portugal Joao Neves, mai shekara 19, wanda ya ki amincewa da tayin kulob din na Portugal. (Record Portuguese)

People are also reading