Home Back

Shugaban rundunar ‘yan sandan Kenya ya yi murabus

dw.com 2024/8/21
Japhet Koome

Shugaban rundunar ‘yan sandan Kenya ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon sukar da aka yi masa kan zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama, a cewar fadar shugaban kasa, wanda shi ne babban  jami'i na baya bayan nan da guguwar zanga-zangar ta yi awon gaba da shi.

Shugaba William Ruto ya amince da murabus din Japhet Koome, babban sufeton 'yan sandan kasar, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.

People are also reading