Home Back

Kotu ta ƙwace kadarorin Naira biliyan 12.1 daga hannun Emefiele, ta maida wa Gwamnatin Tarayya

premiumtimesng.com 5 days ago
RA’AYIN PREMIUM TIMES:  A gaggauta ceto Najeriya daga hannun Emefiele, ɗan ragabza da gidoga

Babbar Kotun Jihar Legas a ranar Juma’a, ta umarci EFCC ta damƙa kadarorin Naira biliyan 12.1 da ta ƙwato daga hannun tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Kadarorin ɓangare biyu ne. Akwai na ƙiyasin Naira biliyan 11.14, sai kuma wasu na ƙiyasin Naira biliyan 1.04.

Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ne ya bada umarnin ƙwacewar a ranar Juma’a, bayan sauraren buƙatar yin ƙwacewar ta ƙarshe daga Hukumar EFCC, bisa jagorancin lauyan ta, Chineye Okezie.

A ranar 5 ta Yuni ne dai kotun ta yi wa kadarorin ƙwacewa ta wucin-gadi, kafin a yi ƙwacewar faufaufau a juya Juma’a. Haka Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito a ranar yau Asabar.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labari a ƙarshen watan jiya, na yadda kotu ta ƙwace Dala miliyan 4.7, Naira miliyan 830, ‘plaza-plaza’, ‘estate-estate’ da gidaje da filaye birjik a hannun Emefiele.

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta ƙwace Dala miliyan 4,719,054 daga hannun tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele. Kuɗaɗen dai sun haura Naira biliyan 6 a masayar canjin kuɗi.

Ba su kenan ba, kotun ta kuma ƙwace Naira miliyan 830,875,611 dukkan su waɗanda aka gano cewa su na kimshe a wasu asusun bankuna, amma kuma mallakar Emefiele ne.

Mai Shari’a Yellim Bogoro ne ya bada umarnin ƙwace kuɗaɗen a ranar Alhamis.

Akwai kuma tulin kadarori da kotun ta ƙwace, baya ga zunzurutun kuɗaɗen.

Kotu ta ƙwace kuɗaɗen daga Emefiele bayan duba buƙatar ƙwacewar da lauyoyin EFCC suka shigar su biyu, wato Bilkisu Buhari da C C. Chinenye.

Daga nan Mai Shari’a Bogoro ya umarci EFCC ta buga sanarwar ƙwace kuɗaɗen a jaridun da ake bugawa a kowace rana.

“A buga sanarwar a jaridu, duk mai jayayya kan ƙwace kuɗaɗen ya zo kotu ya yi bayani.” Inji Bogoro.

Kadarorin da aka ƙwace su na da yawan gaske. Amma dai kuɗaɗen su na ajiye ne a banki da sunan wata mata mai suna Omoile Anita Joy, wadda tuni ta tsere aka neme ta aka rasa. Wasu kuma da sunan Deep Blue Energy Service Limited da sauran su da dama.

Sai a ranar 2 ga Yuli za a yi zaman ƙarshe na ƙwace kuɗaɗen da kadarorin, idan babu wanda ya je kotu ya yi iƙirarin cewa kuɗin sa ko kadarorin sa ne.

Emefiele wanda ke fuskantar tuhuma a kotunan Legas da Abuja, zai rasa tulin kadarorin sa waɗanda EFCC ta riƙe bisa umarni da amincewar kotu.

Daga cikin kadarorin kuwa, akwai dogon bene hawa 11 mai ɗauke da ofisoshi ko ɗakuna 94. Wani bene hawa 11 da kuma wasu birjik a wurare da unguwanni daban-daban a Legas.

People are also reading