Home Back

Sallah: Matawalle Ya Gwangwaje Zamfarawa da Raguna, Ya Raba 390m

legit.ng 2024/7/2
  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya raba raguna 4,860 ga al'ummar jihar domin su gudanar da bukukuwan babbar Sallah na 2024 cikin walwala
  • Ƙaramin ministan tsaron a gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma ware Naira miliyan 390 domin rabawa magoya bayan jam'iyyar APC a jihar
  • Rabon tallafin da tsohon gwamnan ya yi ya haɗa da zaɓo wasu mutum 140 daga ƙananan hukumomi 14 na jihar inda aka ba su N100,000 kowanensu domin bikin Sallah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gabanin bikin Eid-el-Kabir na 2024, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle ya raba raguna 4,860 ga al'ummar jihar.

Ƙaramin ministan ya kuma ware Naira miliyan 390 domin rabawa magoya bayan jam’iyyar APC da masu ƙaramin ƙarfi wanda hakan na daga cikin al’adarsa a lokacin irin waɗannan bukukuwa a jihar.

Matawalle ya raba raguna a Zamfara
Matawalle ya raba N390m domin bikin Sallah a Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle Asali: Facebook

Su za su amfana da tallafin Matawalle?

Jaridar Tribune ta ce waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na jihar da kuma shugabannin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da dattawan jam’iyyar, matasa, ƙungiyoyin mata, malamai, marasa galihu, marayu da gajiyayyu da kuma ƴan jam’iyyar APC a faɗin jihar.

Sauran sun kasance tsofaffin masu muƙami a gwamnatin Matawalle da suka haɗa da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, da manyan daraktoci.

Sauran sune manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman, mambobin hukumomi da sauransu.

Hakazalika, an zaɓo mutane 140 daga ƙananan hukumomi 14 na jihar tare da ba su Naira 100,000 kowannensu domin tallafa musu a yayin bikin Sallah.

Marafa ya caccaki Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu/Shettima 2023 a jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya caccaki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Kabiru Marafa ya caccaki tsohon gwamnan na jihar Zamfara ne kan kiran Dattawan Arewa a matsayin wani nauyi da ya damu ƴan Arewa.

Asali: Legit.ng

People are also reading