Home Back

Kwastam Ta Sake Kama Makamai A Filin Jirgin Saman Legas

leadership.ng 5 days ago
Kwastam Ta Sake Kama Makamai A Filin Jirgin Saman Legas

Kasa da sa’o’i 48 da sanar da kama wata kwantena ɗauke da makamai da aka shigo da su kasar nan ba bisa ka’ida ba daga ƙasar Turkiyya, a tashar jirgin ruwa ta Onne a Jihar Ribas, babban Kwanturolan hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya sanar da sake kama wasu tarin makamai a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Makaman wanda kuɗinsu ya kai Naira miliyan 270, an kama su ne a sashen dakon kaya na tashar jirgin saman, inda bincike ya nuna an shigo dasu ne daga Turkiyya, tare da wani mutum da a yanzu yake a tsare.

A cewar shugaban, jami’ansu da ke filim jirgin sun kuma kama kayan aikin soja da wasu nau’in kayyayakin hukumomi tsaro.

Bisa la’akari da yawan haɗuran da ke tattare da sa ido kan kayan da ake shigowa da su, ya sa hukumar Kwastam ɗin ta wajabatawa kanta nazari sosai kan kwantenonim da ke kawo wa kasar nan.

An gano kwantenar na ɗauke da bindigogi guda 844 da harsasai 112,500 da aka shigo da su cikin kasar nan daga Turkiyya.

People are also reading