Home Back

Tsohuwar Matar Sani Danja Ta Yi Wani Sabon Aure, Mutane Sun Sanya Albarka

legit.ng 2024/6/28
  • Rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta yi sabon aure shekaru uku bayan rabuwar ta da Sani Danja
  • Aminiyar jarumar, Samira Ahmed ce ta tabbatar da hakan a shafinta na Instagram a daren ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024
  • Mutane da dama sun yi tsokaci kan wannan aure na Mansurah Isah wanda babu gayyata, inda wasu suka ce sun so ta koma gidan Danja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rahoto da muka samu daga jarumar fina-finan Hausa, Samira Ahmed na nuni da cewa tsohuwar matar Sani Danja, Mansurah Isah ta yi sabon aure.

Auren Mansurah Isah dai an yi ne makonni biyu bayan da tsofaffin ma'auratan suka aurar da 'yarsu, Riziqat Sani Danja.

Tsohuwar matar Sani Danja, Mansurah Isah
Mansurah Isah ta yi sabon aure bayan shekara 3 da rabuwa da Sani Danja. Hoto: mansurah_isah Asali: Instagram

Samira Ahmed, wadda aminiya ce ga Mansurah Isah ta ba da labarin sake auren tsohuwar jarumar a shafinta na Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waiwaye: Auren Sani Danja da Mansurah Isah

An tafka soyayya ba 'yar kadan ba tsakanin Sani Danja da Mansurah Isah, tun suna fitowa a fim daya ake zargin jaruman na kaunar juna.

Cikin Ikon Allah, jaruman biyu suka amince da juna tare da zama ma'aurata, abin da ya kara masu daraja a masana'antar Kannywood.

A shekarar 2018 ne Sani Danja da Mansurah Isah suka cika shekara 11 da yin aure, amma a shekarar 2021 lamura suka rincaɓe.

Auren Sani Danja da Mansurah Isah ya ƙare

A karshen watan Mayun 2021 ne Mansurah Isah ta shelanta wa duniya cewa aurenta da Sani Danja ya ƙare.

Kamar yadda muka ruwaito a lokacin, tsohuwar jarumar ta ce rabuwar ta da uban 'yayanta shi ne mafi a'ala a gare su baki daya.

Mansurah Isah ta sha suka kan rabuwar ta da Sani Danja, in da har ta ɓa fitowa ta yi 'Allah ya isa' ga wadanda ke zaginta, tana mai cewa ba kanta farau ba.

An yi auren ɗiyar Danja da Mansurah

A cikin watan Mayun 2024 ne Mansurah Isah da Sani Danja suka ƙara haduwa a inuwa ɗaya domin gudanar da bikin babbar 'yarsu Riziqat Sani Danja.

Jarumai, mawaka, da dai sauran 'yan Kannywood sun halarci wannan biki kuma an ga farin ciki a fuskokin tsofaffin ma'auratan.

Kalli bidiyon auren a kasa:

Mansurah Isah ta yi sabon aure

A yanzu da Mansurah Isah ta yi sabon aure, masu mafarkin jarumar za ta iya komawa gidan tsohon mijinta sai su farka.

Samira Ahmed ta ce:

"Alhamdulillah, an daura auren Mansurah Isah yanzu, Allah ya sanya alheri, ya ba su zaman lafiya, Amin."

Kalli sanarwar a ƙasa:

Mutane sun taya Mansurah Isah murna

Mutane sun yi magana game da auren jarumar da aka yi a sirrance ba tare da an shelanta ko an aika wani katin gayyata ba.

1kamalahmad:

"Masha Allah! Allah ya ba su zaman lafiya. Kash! Amma dai mun so ta koma gidan 'yayanta, amma Allah ya riga ya tsara haka."

eesha_dangoggo:

"Masha Allah! Allah ya sanya alkhairi. Allah ya nuna mana naki Aunty samee."

danhalak:

Amman dai baki fada mana ba, da munzo mun taya ta murna. Sai dai Allah ya sa ba ‘auren kisan wuta ba ne’

"Ina cikin damuwa" - Adam A Zango

A wani labarin, mun ruwaito cewa Adam A Zango ya koka kan jarabawar rayuwa da yake ciki da kuma yadda wasu 'yan Kannywood suka juya mashi baya.

Kamar yadda ya wallafa a a shafinsa na Instagram, Zango ya ce burinsa a yanzu ya samu farin ciki ko da kuwa na mako daya ne.

Asali: Legit.ng

People are also reading