Home Back

Jam'iyyar APC Ta Fusata, Ta Umarci Majalisar Dokoki Ta Tsige Gwamna Nan Take

legit.ng 2024/5/19

Jihar Rivers - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ribas ta umarci mambobin majalisar dokokin jihar su fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

APC, wadda ke da mafi rinjaye a majalisar, ta umarci mambobin ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule su fara bin matakan doka na tsige Gwamna Fubara nan take.

Gwamna Fubara na jihar Ribas.
Jam'iyyar APC ta fusata da kalaman Gwamna Fubara kan sulhun rikicin siyasar jihar Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara Asali: Facebook

Kwamitin riƙon kwarya na jam'iyyar APC karƙashim jagorancin shugaban kwamitin, Tony Okocha, ne ya sanar da haka a Fatakwal ranar Talata, 7 ga watan Mayu.

Jam'iyyar APC ta yi kira da a tsige Fubara ke biyo bayan kalaman da ya yi kam sulhun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi a rikicin siyasar jihar.

Idam zaku iya tunawa, shugaba Tinubu ne ya jagoranci yayyafawa wutar rikicin ruwan sanyi a wani taro da ya kira a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a ƙarshen makon nan, Gwamna Fubara ya bayyana cewa wannam sulhum ba doka ba ce, sulhu ne na siyasa domin kawai a zauna lafiya.

Gwamna Fubara ya kuma ƙara da cewa idan da ya so da tuni ya rushen majalisar dokokin jihar domin doka ba ta san da zamansu ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading