Home Back

Ko Kin San… Sirrin Hulba Ga Mace?

leadership.ng 2024/8/21
hulba

Assalamu alaikum masu karatu barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.

 

A yau shafin na mu zai zo muku da amfanin Hulba:

Ana amfani da Hulba wajen maganin cushewar ciki; Hulba na taimakawa wajen saurin narkewar abinci, sakamakon haka ne ta ke maganin cushewar ciki. Duk ma su fama da matsalar cushewar ciki ko kumburin ciki sakamakon rashin narkewar abinci sai ya dimanci amfani da Hulba, zai samu sauki in sha Allahu.

Sannan ana amfani da Hulba don karin ni’ima, Idan mace na fama da rashin ni’ima ko bushewar farji, za ta iya samun Hulba ta yi amfani da ita, kuma in sha Allahu za ta dace:

Yadda za ki hada:

Idan kina so ki yi amfani da Hulba don karin ni’ima, sai ki samu ‘ya’yan Hulba da kanumfari da ‘ya’yan Habbatus-sauda da kuma Zuma mai kyau.

Za ki hada ‘ya’yan Hulba da na habbatus sauda da kanumfari waje guda ki dafa su, idan sun dafu sai ki sauke ki jira ya huce, sannan sai ki zuba zumar a ciki, ki dinga sha. In sha Allahu za ki sha mamaki.

Hulba na taimakawa wajen rage kiba da teba. Ki yawaita sanya ta a cikin girkinki kowanne a abinci za ki yi ki rika zuba ta a ciki yana rage kiba da tumbi.

People are also reading