Rundunar 'Yan Sanda Ta yi Tir da Yadda Aka Yiwa Sarkin Kano Ihu Yayin Hawan Sallah
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Rundunar 'yan sanda ta bayyana fushinta ga wadanda su ka yi ihu ga sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ihu bayan ya dawo daga sallar idi a hanyarsa ta komawa fada.
Kamar yadda aka saba a al'ada, sarkin Kano kan sauya hanya bayan ya idar da sallar idi, a nan ne sarki Sanusi II ya bi ta Zage/Zango kuma a nan ne aka ji wasu na yi masa ihu.
Vanguard News ta wallafa cewa a sanarwar da jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu, ya ce 'yan sanda ba za su lamunci rashin da'a ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar yan sandan Kano ta gargadi masu niyyar kawo tarzoma jihar su kuka da kansu, domin an kammala shirin dakile dukkanin barazanar tsaro a fadin jihar, kamar yadda Solace Base ta wallafa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya yi gargadin, inda ya kara da cewa su na sanya idanu kan bukukuwan sallah a jihar domin tabbatar da tsaro.
SP Kiyawa ya kuma yi gargadin masu fita bukukuwan sallah da ka da su rika yawo da makamai, domin za a duba abubuwan hawa sosai a kokarin ganin ba a samu tashin hankali a Kano ba.
A baya mun kawo mu ku labarin yadda sarkin Kano na 16 ya yi fatali da umarnin rundunar 'yan sanda inda ya gudanar da bikin hawan sallah babba a masarautarsa.
Tun da fari rundunar 'yan sanda ta hana hawan sallah biyo bayan dambarwar da ta dabaibaye masarautar Kano yayin da ake ci gaba da shari'a domin tabbatar da waye sarki.
Asali: Legit.ng