Home Back

Digiri vs Kwarewa: Maganar Firaministan Birtaniya Ta Tayar da Kura a Intanet

legit.ng 2024/7/5
  • Firaministan kasar Birtaniya ya bayyana cewa samun nasara a rayuwa ba sai mutum ya mallaki kwalin digiri ba a yanzu
  • Sai dai maganar ta tayar da kura a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta ta yadda ake bayyana ra'ayoyi mabanbanta
  • Ƴan Arewa sun bayyana ra'ayinsu game da batun musamman lura da muhawara da aka yi kwanan tsakanin digiri da kwarewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Firaministan kasar Birtaniya, Rishi Sunak ya wallafa wani sako da mutane ke kallon ragewa masu kokarin mallakar kwalin digiri karfin gwuiwa ne.

Firaministan ya bayyana cewa a zamanin yanzu, ba lallai sai mutum ya mallaki digiri ba zai samu nasara a rayuwa.

Birtaniya
Maganar Rishi Sunak kan digiri ta ja hankula a intanet. Hoto: Rishi Sunak Asali: Facebook

Firaminista Rishi Sunak ya wallafa sakon ne a shafinsa na Facebook a jiya Laraba, 29 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin da aka yiwa Rishi Sunak

Kar ku manta Rishi ya mallaki digiri!

Cikin martanin da Dakta Adamu Tilde ya yi a kafar Facebook, ya ja hankalin matasa kan cewa kada su rudu da kalaman Firaministan saboda shi kansa ya mallaki kwalin digiri daga manyan jami'o'in duniya.

Tilde

Dakta Tilde ya kara da cewa ya kamata duk wanda yake da dama ya mallaki digirin farko domin hakan zai bude masa wasu hanyoyin samun nasara a rayuwa.

Zan karfafi mutane su yi digiri

Malam Zaharadden Ibrahim ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa duk da bai samu damar zuwa jami'a ba, amma zai cigaba da karfafan yan baya a kan mallakar kwalin digiri.

Ya ce daga cikin hanyoyin samun nasara a duniyar yau akwai zuwa jami'a kasancewar za ta ba mutum wayewa da sanin yadda zai tafiyar da rayuwa a zamanance.

Digiri ba takardar tsire ba ne

Qaanso Bari ta wallafa martani a shafinta na Facebook kan cewa ba lallai ba ne mutum sai ya samu digiri kafin ya yi nasara a rayuwa.

Amma ta yi gargadi kan masu kushe digiri suna ganin kamar ba shi da bambanci da takardar tsire. Ta ce digiri na da alfanu sosai a rayuwar yau.

An bude tashar zamani a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa an bude sabuwar tashar zamani wacce motoci sama da 5,000 za su rika hada hada daga sassan Najeriya a jihar Gombe.

Ministan sufuri, Sa'idu Ahmed Alkali ne ya bude tashar a ranar Talata, 28 ga watan Mayu kuma an rada mata sunan tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo.

Asali: Legit.ng

People are also reading