Home Back

Ƴansanda sun hana cin Kasuwar Wuse a Abuja, tsawon kwanaki biyu bayan tashin hargitsi

premiumtimesng.com 2024/4/30
HARGITSIN ABUJA: Yadda matasa suka yi wa Ofishin ƳanSandan Kasuwar Wuse rubdugu, suka ƙona motoci, bayan jami’in tsaro ya bindige ɗan talla

Tun a ranar Laraba ce jami’an Ƴansanda suka kulle babbar kasuwar Abuja da ke Wuse, kwana ɗaya bayan ɓarkewar hargitsin da ya yi sanadiyyar ƙone wasu kantina da farfasa ofishin ‘yan sanda.

Hargitsin ya ɓarke bayan wani jami’in tsaron gidan kurkuku ya bindige wani ɗan talla, wanda ya nemi tserewa kan hanyar tafiya da su gidan kurkuku, bayan yanke masu hukunci da wata kotun tafi da gidan ka ta yi masu a cikin kasuwar.

Wakilin mu ya ji cewa a ranar Laraba ‘yan kasuwa da kwastomomi sun shiga cikin kasuwar har an fara hada-hada kamar tsawon sa’o’i uku, sai kuma ‘yan sanda suka ce kowa ya fita.

Haka dai wani mai kanti a cikin kasuwar, mai suna Alhaji Babangida ya shaida wa wakilin mu.

“Har yau Alhamis ɗin nan da na ke magana da kai ba a buɗe kasuwar ba. Ban sani ba ko an bar masu kayan Gwari, ko nama ko kayan da ka iya lalacewa sun shiga domin su gyara kayan su. Saboda na je na ga kasuwar a rufe, amma ban matsa kusa da ƙofar shiga ba.” Inji Babangida.

PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda hasalallun matasa suka yi wa Ofishin ‘Yan Sandan Kasuwar Wuse rubdugu, sun ƙone motoci, bayan jami’in tsaro ya bindige ɗan talla.

Fitacciyar Kasuwar Wuse da ke tsakiyar Babban Birnin Tarayya, Abuja ta hargitse da yammacin ranar Talata, yayin da hasalallun matasa suka kai wa Ofishin ‘Yan Sanda na kasuwar farmaki, har suka ƙone motoci, huce-haushin kisan wani ɗan talla da wani jami’in tsaro ya yi.

Hargitsin ya yi sanadiyyar tashin gobara a wasu kantina 10 kuma aka ƙone motoci 8 duk a ranar Talata a kasuwar.

Shaidar ganin abin da ya faru ganin idon sa, ya shaida cewa wani ɗan talla ne da ‘yan sanda su ka ce sunan sa Ibrahim Yahaya mai shekaru 27 aka bindige, bayan jami’an tsaron ‘task force’ masu kamen ‘yan talla tare da ‘yan sanda sun kama shi.

An ce ɗan tallar wanda aka bindige, ƙoƙarin gudu ya yi daga hannun su. Haka dai wasu masu kantina da suka ga yadda lamarin ya faru suka shaida.

Wannan kisa da aka yi wa ɗan talla, ya harzuƙa hasalallun dandazon matasa a cikin kasuwar, wadda a kullum cike ta ke danƙam da ‘yan dako da ‘yan tallar da ke yawo da kayan sayarwa a hannu.

Hasalallun sun da farko sun dumfari ofishin ‘yan sanda da ke kasuwar, suka farfasa tagogi, sannan suka banka wa motocin da ke ajiye gaban ofishin wuta. Kusan motoci 8 ne aka banka wa wuta a lokacin da hargitsin ya ɓarke wajen ƙarfe 3:30 na yamma.

Ƴansanda sun yi amfani da barkonon-tsahuwa suka tarwatsa matasan, kamar yadda wani ya tabbatar.

Kimanin kantina 10 ne wuta ta kama yayin hargitsin.

Wasu masu kantina dai sun ɗora alhakin tashin gobarar da ta ci kantinan su da tashin barkonon-tsohuwar da ‘yan sanda suka riƙa harbawa.

Wani mai kanti mai suna John Abasi ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa: ‘Gaskiyar magana barkinon-tsuhuwa da ‘yan sanda suka riƙa harbawa ne ya haddasa masu gobara.

“Ka san kuma idan aka ce maka an kashe wani, jama’a za su hasala su harzuƙa. To sai mutane suka yi ƙoƙarin afka wa wanda ya yi harbin da ya kashe ɗan tallar, amma dai ya tsere. Sai suka fara lalata kayan sa. Dalili kenan suka ƙone motocin can.

“Daga nan sai ‘yan sanda suka fara harba barkonon-tsohuwa, wanda ya riƙa dira cikin kantinan mutane wuta ta riƙa tashi ta na ƙone masu kayayyaki.”

Wani rahoton kuma ya ce Jami’an Hukumar Kula da Kasuwannin Abuja (AMML) da ke cikin kasuwar sun tabbatar da an harbi ɗan tallar, kuma kisan sa ne ya haifar da ɓarkewar hargitsin har mafusata suka banka wa kantina wuta. An ce ofishin jami’an AMML shi ma an banka masa wuta.

Rundunar ‘Yan Sandan Abuja sun tabbatar da faruwar lamarin da aka kashe Ibrahim Yahaya mai shekaru 27.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce ba ɗan sanda ne ya bindige ɗan tallar ba.

Ta ce mamacin dai wani jami’in tsaron gidan kurkuku ne ya bindige shi lokacin da ya yi ƙoƙarin gudu daga hannun su.

Bayanin ta ya ce: “Binciken farko ya tabbatar da cewa an kama wani mai suna Ibrahim Yahaya ne mai shekaru 27, kuma jami’an kamen ‘yan talla ne suka kama shi, wato ‘task force’. Sun gabatar da shi a wata kotun tafi-da-gidan-ka wadda ke zama a cikin Kasuwar Wuse a kowace ranar Talata.

“An yanke masa hukunci shi da wasu. To ana tafiya da su zuwa kurkuku ne sai ya diro daga cikin motar da ke ɗauke da su ya fara gudu. To sai wasu jami’an kurkuku biyu da ke cikin motar su ka bi shi a guje, har ɗaya ya bindige shi.

“Sun ce an garzaya da shi asibiti da ke kusa, inda likitoci suka tabbatar da ya mutu.”

 
People are also reading