Home Back

Tsaro: Gwamnoni Arewa Maso Yamma Za Su Yi Taro Domin Neman Mafita A Katsina

leadership.ng 6 days ago
Tsaro: Gwamnoni Arewa Maso Yamma Za Su Yi Taro Domin Neman Mafita A Katsina

Gwamnonin Arewa Maso Yamma haɗin gwiwa da hukumar UNDP za su shirya wani taron neman mafita a kan matsalar tsaro da yankin ke fama da ita shekara da shekaru.

Taron wanda ake sa ran shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu zai buɗe a ranar Litinin na da nufin tattaunawa da kuma lalubo hanyar da za a magance wannan matsala.

Taken wannan taro dai shine ‘Haɗin kan yanki domin ceton rayuka da kuma dukiyoyin al’umma”

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai a Katsina kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Hon. Salisu Bala Zango ya bayyana cewa wannan taron irin sa na farko za a yi a tarihi.

Ya ƙara da cewa gwamnoni da masu ruwa da tsaki da masana daga yankin arewa maso yamma za su taro domin tattaunawa ta musamman da nufin samar da mafita akan sha’anin tsaro.

A cewar sa, matsalar ta kai matsala ta yadda ‘yan bindiga sun hana yankin arewa maso yamma yin noma, wanda hakan ke bada gudunmawa wajen shiga kuncin rayuwa da kuma yunwa a yankin arewa da ƙasa baki ɗaya.

“Wannan taro zai maida hankali wajen ganin jihohin Kaduna da Kano da Katsina da Kebbi da Sokoto Jigawa da kuma Zamfara sun samu mafita domin yin barci da idanu biyu.” Inji shi

Kwamishinan wanda ya ƙara da cewa taron kachokam zai maida hankali ne wajan samar da yanayin mai kyau akan matsalar tsaro da kuma duba da hanyar samar da zaman lafiya mai ɗorawa ta hanyar haɗa hannun a tsakanin gwamnoni yankin.

Dakta Salisu Bala Zango ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya da gwamnonin arewa maso yamma da hukumar UNDP za su yi tattaunawa ta ilimi wajen samar da mafita a wannan yanki da matsalar tsaro ta kasra shi.

“Sannan a ƙarshen taron za a fito da musababbin matsalar tsaro da kuma tabbatar da haɗin kan jami’an tsaro da ƙoƙarin tabbatar da ingancin tsaro da hanyar za a taimakawa waɗanda bala’in ‘yan bindiga ya shafa” inji Kwamishina

Za dai a fara wannan taro a ranar Litinin a kammala ranar talata tare da fatan cewa taron zai haifar da ɗa mai ido, domin an sha yin tarurruka akan sha’anin tsaro daga baya kuma aji shiru.

People are also reading