Home Back

Cika shekaru 30 da jingine dokar hukunta neman jinsi a Jamus

dw.com 2024/8/21

 A karni na 19, an tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda aka kama da laifin mu'amala a tsakanin jinsi guda har ma da zaman kaso na watanni shida. Sai dai tun a shekarar 2017, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta halarta auren jinsi. Amma a cewar Patrick Dörr guda daga cikin shugabannin masu neman jinsi a Jamus, kasar ta yi latti wajen kawar da wannan bambanci a tsakanin al'umma da ke da 'yanci. 

Karin bayani: Ranar tuni da kare hakkin masu neman jinsi

 Patrick Dörr ya ce: " A shekarar 1994, Jamus kasa ce da ba a tattauna batun mu'amalar jinsi guda, ko da kuwa a makarantu ne. A tasowata, ban san mutum ko daya da ya kasance dan luwadi ba, kwata-kwata babu mutane daga cikin al'umma da za ka kalla ka ce wannan gwarzona ne ko abin sha'awata ne har ma a fannin watsa labarai. Sai dai za a iya cewa duk wadannan sun kau kuma ci-gaba ne da muke alfahari da shi"

Wannan doka mai sakin layi 175 ta samo asali ne a lokacin mulkin 'yan Nazi, don hukunta duk wasu dabi'u na neman jinsi da a wancan lokacin kan kai mutum har ya zuwa gidan yari na kusan shekaru 10. Kusan mutane dubu 100 ne masu neman jinsi aka kora daga kasar, yayin da aka kai wasu gidan yari yayin da ake azabtar da wasu. Sama da shekaru 120 ne rayuwar masu neman jinsi a Jamus ta kasance cikin tsananin kunci.

 Patrrick Dörr ya kara da cewa: "An fara gabatar da dokar hadin gwiwar farar hula a karkashin gwamnatin ja-kore a shekara ta 2001, sannan a hakika an gabatar da auren kowa a karkashin Angela Merkel a cikin 2017. An sami jinsi na uku a cikin rajistar matsayin farar hula tun 2018. Kuma kwanan nan. an kuma zartar da dokar ta-da-kai, wanda kuma ke baiwa masu yin jima'i da jima'i damar yanke shawara."

Karin bayani: Faretin 'yan luwadi da madigo a Kolon

Wannan doka ta sanya Jamus cikin jerin manyan kasashen yammacin duniya da suka dade da aiwatar da dokar daina hukunta masu neman jinsi.  duk da cewar tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ba ta yi maraba da matakin ba. 'Yan Majalisar dokoki kimanin 393 ne suka amince da dokar ta auren jinsi guda, sannan 226 kuma suka watsi da ita, yayin da hudu  suka yi rowar kuri'arsu.