Home Back

Shugaban CMG Ya Aike Da Wasika Ga Wata Ba’amurkiya Abokiyar Sinawa

leadership.ng 2024/6/29
Shugaban CMG Ya Aike Da Wasika Ga Wata Ba’amurkiya Abokiyar Sinawa

A bana, bikin gargajiya na Sin wato bikin Duanwu, ya zo daidai ranar tattauna harkokin wayewar kan duniya, wadda MDD ta samar. A jiya Litinin 10 ga watan nan na Yuni, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Chicago na kasar Amurka, sun shirya wani aiki mai taken “Ziyara gidan tsohuwar abokiyar Sinawa”, a gidan malama Sarah Lande, wata Ba’amurkiya abokiyar al’ummar Sinawa dake zaune a birnin Muscatine.

Shugaban CMG Shen Haixiong, ya aike da wasika ga malama Sarah Lande, wadda a ciki ya rubuta cewa, “CMG yana son yin aiki tare da ke, da ma sauran abokan Sin na Amurka, don gina gada mai karfi ta inganta fahimtar juna, da musayar al’adu tsakanin Sin da Amurka. (Safiyah Ma)

People are also reading