Home Back

Mutane 8 Sun Mutu Yayin da Aka Yi Asarar Dukiyar da Ta Kai N31.6m a Jihar Kano

legit.ng 2024/7/4
  • An rasa rayukan mutum takwas kuma kadarorin da suka kai na N31.6m sun salwanta a ibtila'in gobara a jihar Kano cikin watan Mayu
  • Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi ne ya faɗi haka da yake jawabi kan ayyukan hukumar a watan jiya
  • Ya shawarci mutane su riƙa kokarin kai ɗauki idan wuta ta kama, sannan ya gargaɗi direbobi su yi tuki da taka tsan-tsan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar kashe gobara da jihar Kano ta bayyana matsalolin tashin gobarar da ta fuskanta da asarar da mutane yi cikin watan Mayun da ya gabata a jihar.

Hukumar ta ce lamarin gobara kala daban-daban da suka faru sun yi ajalin mutane takwas tare da lalata kadarorin da kudinsu ya kai Naira miliyan 31,650,700 a watan Mayu.

Taswirar jihar Kano.
Gobara ta zama ajalin mutum 8 a jihar Kano a watan Mayu, 2024 Asali: Original

Mai magana da yawun hukumar na jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jami'an kwana-kwana sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa daban-daban a tashohin ƴan kwana-kwana 29 a watan Mayun 2024.

Saminu ya ce kira-kirayen da suka samu sun haɗa na kawo rahoton tashin wuta guda 51, na neman ɗauki 13 da kuma sanarwar ƙarya guda shida.

"Ƙiyasin kaddarorin da gobara ta lalata a cikin watan Mayu sun kai N31,650,700, yayin da ƙiyasin kimar kadarorin da jami'an kashe gobara na jihar suka ceto ya kai N98,700,000.
"An rasa rayukan mutane takwas yayin da jami'ai suka samu nasarar ceto mutum 10."

Abdullahi ya bukaci ɗaukacin al'umma da su yi taka-tsan-tsan wajen ƙoƙarin ƙai ɗauki da kashe gobara domin daƙile barna kafin isowar jami'an hukumar.

Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rika tuƙi a hankali tare da bin dokokin hanya domin gujewa hadurra.

A wani rahoton na daban Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama fitaccen dan TikTok , G-Fresh Al'ameen saboda zargin yi wa Al-Kur'ani izgili.

Babban daraktan Hisbah na jihar, Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar da kama G-Fresh ga manema labarai a ranar Lahadi da ta gabata.

Asali: Legit.ng

People are also reading