Home Back

Bola Tinubu Zai Miƙa Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Ga Majalisar Tarayya

legit.ng 2024/7/3

FCT Abuja - Mai girma shugaban ƙasa ya ce zai miƙa kudin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisar tarayya nan ba da jimawa ba.

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya yiwa ƴan ƙasa a ranar Demokuraɗiyya, 12 ga watan Yuni, 2024.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa ya ce zai tura kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisar tarayya Hoto: Bayo Onanuga Asali: Twitter

Tinubu ya ce yana sane da wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta kuma ya buƙaci su daure, sannan su jajirce wajen ƙara tabbatar da tsarin demokutaɗiyya.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a yau Laraba, 12 ga watan Yuni, Najeriya ta cika shekaru 25 da dawowar demikuraɗiyya ba tare da samun tangarɗa ba.

Idan baku manta ba a ranar Litinin da ta wuce, kwamitin mafi karancin albashi karƙashin jagorancin Alhaji Bukar Goni Aji ya miƙa rahoto bayan kusan watanni biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakilan gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun miƙa tayin N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Sai dai ƙungiyar kwadago ta ƙasa ta rage buƙatarta daga N494,000 zuwa N250,000 a zaman kwamitin na ƙarshe.

Bayan karɓan rahoton ana sa ran Mai Girma Tinubu zai ɗauki matsaya kana ya miƙa kudirin dokar sabon albashi ga majalisar tarayya domin ta amince da shi.

Da yake jawabi yau, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ɗauko shi ne mafita a kokarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.

"Tattalin arzikinmu ya jima yana buƙatar gyara tsawon shekaru, saboda bai zama daidai ba, an dogara kan man fetur ne kaɗai wajen samun kuɗin shiga.

"Mun ɗauko wannan tsare-tsare ne domin gina makomai mai kyau ga ƙasarmu, duk da suna tattare da wahala amma ya zama wajibi mu jure."

Asali: Legit.ng

People are also reading