Home Back

Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yin Katsa-landan A Harkokin Kano

leadership.ng 2024/7/1
Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC da daukar matakan da ba su dace a kan sha’anin harkokin Kano ba. 

Kwankwaso, ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da aikin titin Madobi mai tsawon kilomita 82 a garin Madobi.

Tsohon gwamnan na Kano, kuma jagoran gwamnatin jihar, ya bayyana cewa al’ummar Kano ba za su lamunci duk wani yunkuri na katsa-landan a sabgar da ta shafi jiharsu ba.

Ya kuma jaddada aniyar ‘yan Jihar Kano na mara wa gwamnanatin Kano baya duk da tsoma bakin da gwamnatin tarayya ke yi.

Kwankwaso, yayin da yake jawabi ga wadanda ya bayyana a matsayin makiyan jihar, ya soki gwamnatin tarayya da daukar tsauraran matakai, kamar son kafa dokar ta-baci a Kano da sauransu wajen hana Jihar ci gaba.

Kwankwaso ya shawarci gwamnatin tarayya da ta yi hattara da ’yan siyasa marasa kishin kasa daga Kano, yana mai gargadin cewa irin wannan kawancen ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

People are also reading