Home Back

Sojoji Da Mafarauta Sun Dakile Shirin ‘Yan Ta’adda Na Lalata Falwayar Wutar Lantarki A Yobe

leadership.ng 2024/8/22
Sojoji Da Mafarauta Sun Dakile Shirin ‘Yan Ta’adda Na Lalata Falwayar Wutar Lantarki A Yobe

Dakarun haɗin guiwa na ‘Operation Hadin Kai’ daga Arewa maso Gabas, sun dakile wani shiri da ‘Yan Boko Haram suka yi na lalata wutar lantarki a garin Kasesa da ke kusa da yankin Damaturu.

Sojojin sun samu nasarar ne tare da hadin guiwar kungiyoyin mafarauta a jihar.

Mai rikon mukamin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kaftin Naziru Shehu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Damaturu a ranar Lahadi.

Naziru ya bayyana cewa hadin guiwar sojojin na ‘Combat Team (CT) 7 na 27’ sun gudanar da wannan aikin a ranar Asabar bayan sun samu sahihin bayanan sirri kan shirin ‘yan ta’addar na lalata wutar yankin.

“Bayan samun bayanan sirri na ayyukan ‘yan Boko Haram, sojoji sun yi nasarar yi wa ‘yan ta’addar kwantan ɓauna cikin hanzari.

“’Yan ta’addar sun gudu sun bar wata mota kirar Toyota Corolla, da suka shirya na’urorin fashewar bama-bamai a cikinta, da nufin tayar da abubuwan fashewa don su lalata wutar lantarkin, sojoji sun yi nasarar buɗe musu wuta da fatattakar su,” in ji Shehu.

Kakakin ya ce babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja da Kwamandan rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai, Maj.-Janar W Shaibu, sun yabawa mazauna yankin bisa hadin kan da suka bayar.

Ya kuma bukaci jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro a kodayaushe kan motsin duk wani abu da ba su gamsu da shi ba.

People are also reading