Home Back

Gwamnatin Kano ta musanta rade – radin da ke cewar ta ware naira biliyan shida domin ciyarwa a watan Ramadana.

dalafmkano.com 2024/5/10

Gwamnatin jihar kano ta ce zancen da ke yawo na cewar ta ware naira biliyan shida domin ciyarwa a watan ramadana ba gaskiya bane.

Engr Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan ta bakin Babban Daraktan yada labaransa Sunusi Bature Dawakin Tofa yayin zantawa da manema labarai, inda ya ce gwamnati ta lamuncewa kwamatin aikin ciyarwar naira biliyan daya da miliyan dari da casa’in da dubu dari bakwai da casa’in ne (1,190,790,000,00).

Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce wannan shine kudin da gwamnatin kano ta ware karkashin jagorancin Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusif, domin ciyar da masu bukata ta musamman da marayu da wa’yanda bazasu iya ciyar da kansu ba a wannan wata na ramadana.

Dawakin Tofa ya kara da cewa, tini ciyarwar ta fara a cibiyoyi guda dari da ke kananan hukumomi takwas da ke kwaryar birnin kano, inda kowacce cibiya zata ringa ciyar da mutum dubu daya a kowacce rana har zuwa karshen watannan ramadana, kamar yadda wakilinmu Abba Haruna Idris ya rawaito mana.

People are also reading