Home Back

Majalisar Dattawa Ta Yi Wa Tinubu Gata, Ta Amince Ya Naɗa Shugaban Hukumar SEC

legit.ng 2024/6/26
  • Majalisar dattawa ta amince da nade-naden da Shugaba Bola Tinubu ya yi a hukumar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya (SEC)
  • Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Emomotimi Agama a matsayin babban darakta na hukumar tare da kwamishinoni uku
  • Mataimakin shugaban majalisar, Barau Jibrin, ya bukaci wadanda aka nada da su yi aiki tukuru domin farfado da tattalin arziki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Emomotimi Agama a matsayin babban darakta na hukumar hada-hadar hannayen jari (SEC).

Majalisar dattawa ta yi zama a Abuja
Majalisar dattawa ta amince da naɗin shugaban hukumar SEC. Hoto: @NGRSenate Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin ne bayan Osita Izunaso, shugaban kwamitin majalisar kan kasuwannin hannun jari na kasar ya gabatar da rahoto.

Majalisa ta amince da nade-naden Tinubu

Sanata Izunaso, ya ce wadanda Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da sunayen su sun cika sharuddan sake bukata domin nada su mukaman in ji rahoto The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda majalisar dattijai ta tabbatar da nadin su a hukumar SEC sun hada da Frank Chukwuogor, matsayin kwamishinan zartarwa (fannin shari'a).

Sauran sun hada da: Abimbola Ajomale, matsayin kwamishiniyar gudanarwa (fannin ayyuka); da Samiya Usman, babbar kwamishiniya (fannin ayyukan kamfanoni).

Majalisa ta gargadi sabbin shugabannin SEC

Jaridar Vanguard ta ruwaito bayan gabatar da rahoton Sanata Izunaso, majalisar dattawa ta kada kuri’a tare da tabbatar da nadin wadanda aka tantance.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya bukaci wadanda aka nada da su gudanar da ayyukansu da kyau domin ci gaban kasar.

Sanata Jibrin ya ce:

"Muna kira a gare su da su yi aiki domin farfado da tattalin arziki, su guji yin wani abu da zai nuna kuskuren shugaban kasar da ya ba nada su mukaman."

Majalisar wakilai ta dura kan NLC

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta zargi shugabannin ƙwadago da yada labaran karya game da albashin 'yan majalisun tarayya domin harzuka jama'a.

Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya ce labaran karya da NLC ke yadawa yana zama cin mutunci ga majalisar.

Hon. Akin Rotimi, ya ce ya kamata 'yan kwadago su daina yada wadannan karairayin a yayin da majalisar ke nuna goyon bayanta ga inganta albashin ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

People are also reading