Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadago Sun Caccaki Gwamnonin Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun caccaki gwamnonin Najeriya 36 kan cewa ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba.
Ƙungiyoyin ƙwadagon sun bayyana kalaman na gwamnonin kan ma'aikata a matsayin mugunta yayin da suka buƙace su da su sake tunani.
A ranar Juma'a ne dai ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Hajiya Halimah Salihu Ahmed ta ce ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake martani kan kalaman gwamnonin, daraktan yaɗa labarai na NLC, Benson Upah, ya ce gwamnonin sun manta da yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar nan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya yi nuna da cewa gwamnonin sun manta da yadda farashin man fetur, Dala da sauran abubuwa suka yi tashin gwauron zabi.
"Mun damu matuƙa kan kalaman da suka fito daga ƙungiyar gwamnoni cewa gwamnonin jihohi ba za su iya biyan N60,000 a matsayin mafi karanci albashi ba saboda wasu jihohin za su riƙa ciyo bashi domin biyan albashi a kowane wata."
"Mun yi amanna cewa abin da gwamnonin suka yi bai dace ba. Bai kamata waɗannan kalaman su fito ba yayin da ake tsakiyar tattaunawa. Sam hakan bai dace ba."
- Benson Upah
Ƴan ƙwadagon sun bayyana cewa kuɗaɗen da ake ba gwamnonin daga asusun gwamnatin tarayya sun ƙaru daga N700bn zuwa N1.2trn wanda hakan ya sanya lalitarsu ta cika yayin da talakawa ke shan wuya.
A cewarsu abin da gwamnonin ya kamata su yi domin su iya biyan mafi ƙarancin albashi (ba N60,000 ba) shi ne su rage kashe kuɗaɗe a gwamnati, rage cin hanci tare da ɗaukar walwalar ma'aikata da muhimmanci.
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe, ya caccaki dokar mafi karancin albashi ta ƙasa.
Okupe ya soki dokar bisa wajabtawa gwamnonin jihohin Najeriya 36 su riƙa biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi a jihohinsu daidai da na gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng