Home Back

Faɗuwar darajar Naira ya haifar da tsada da hauhawar farashin magunguna – Ministan Lafiya

premiumtimesng.com 2024/5/18
DANNE HAƘƘIN MARASA LAFIYA: Majalisa na neman yadda aka yi da Dala miliyan 300, da aka ciwo bashi da nufin ayyukan daƙile cutar zazzaɓin cizon sauro

Ministan Kiwon Lafiya da Walwalar Jama’a, Umar Pate, ya danganta tsadar magunguna da hauhawar farashin su, cewa faɗuwar darajar Naira ce ta haifar da hakan a Najeriya.

Pate ya bayyana haka a ranar Talata, tare da cewa faɗuwar darajar Naira na shafar masu masana’antun haɗa magunguna, saboda ba su iya sawo sinadaran haɗa magungunan da sauran kayan haɗi, domin haɗa magunguna a Najeriya.

A taron wanda gidan Talabijin na Channels ya shirya a intanet, an yi shi ne domin murnar cikar talbijin ɗin shekaru 10 da kafuwa.

Sauran matsalolin da ke haddasa tsadar magunguna a Najeriya, a ta bakin Minista Pate, sun haɗa da tsadar kuɗaɗen lodi, jigila da safarar maganin, tsadar kayan inganta fasaha da kuma ƙa’idojin da ke tattare da harkokin haɗa magunguna.

Shugaban taron kuma tsohon Ministan Lafiya, Julius Adelusi-Adewuyi, ya jaddada muhimmancin bunƙasa masana’antun haɗa magunguna a ƙasar nan, sai kuma ƙara narka kuɗaɗe a harkokin haɗa magunguna.

Ita ma Shugabar Daraktar NAFDAC, Moji Adeyeye, ta bayyana cewa hanyoyin da za a bi domin daƙile matsalar ficewar da manyan kamfanonin haɗa magunguna ke yi daga ƙasar nan, su ne a samu ƙarin masana’antu a cikin gida waɗanda za su riƙa haɗa magunguna.

“Saboda muna buƙatar darajar Naira ta tsaya da ƙafafuwan ta a kasuwar musayar kuɗaɗe. Amma babu abin da kamfanonin waje za su haɗa wanda mu na mu na cikin gida ba za su iya haɗawa ba.

“Abin shaƙar iska na ‘inhaler’ ne kaɗai ba za a iya haɗawa a Najeriya ba,” inji ta.

Pate ya ce masu inshorar lafiya a Najeriya ba su kai kashi 10 bisa 100 ba. Ya ƙara da cewa batun inshorar kiwon lafiya a Najeriya ya daɗe ya na fuskantar ƙalubalen rashin wadatattun kuɗaɗe daga gwamnati, tsawon shekaru 40.

“Da yawan mu za mu afka cikin talauci da ƙarewar dukiyoyin mu idan munanan cutuka irin kansa ko ciwon ƙoda suka kama mu, saboda babu da tsarin inshorar lafiya.” Inji Minista.

People are also reading