'Yan Bindiga Sun Yi Aika Aika a Imo, Sun Kashe 'Yan Sanda da Farar Hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Imo - An wayi gari cikin ɗar-ɗar yayin da wasu yan bindiga suka kai hari kan jami'an tsaro a jihar Imo.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun kai hari ne kan jami'an yan sanda yayin da suke cikin aiki.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an kai harin ne a daidai hanyar Ama-John da ke Okigwe a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa yan bindigar sun yi kwanton ɓauna ne a safiyar yau suka afka kan jami'an yan sanda.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun yi nasarar kashe yan sanda biyu da wani farar hula daya yayin harin.
Wani mutum da ya shaida lamarin yace a yanzu haka mutane sun watse a wurin da aka kai harin, rahoton the Cable.
Mutumin ya ce duk da kasancewar wurin ana hada-hada sosai amma ko masu abubuwan hawa sun taƙaita bin hanyar.
Yayin da aka tuntubi yan sandan jihar, kakakin rundunar, Henry Okoye ya ce bai samu karin haske ba a lokacin.
Yan bindigar su hudu sun kai harin ne a cikin wata mota kirar Sienna Toyota kuma sun arce bayan aikata ta'addancin.
A wani rahoton, kun ji cewa jami'an hukumar kwastam sun kama masu safarar mai a iyakokin Najeriya daga sassa daban-daban na kasar.
Shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi ya bayyana adadin man fetur da suka kwato da kuma yadda masu safarar ke barazana ga tsaron kasa.
Asali: Legit.ng