Home Back

Tinubu ya ce a binciki kwangilolin titinan da ya gada domin tantance gaskiya daga ‘lissafin-dawakan-Rano’

premiumtimesng.com 2024/8/22
GARGAƊIN TINUBU GA TSAGERUN KUDU DA NA AREWA: ‘Za mu tarwatsa duk mai neman tarwatsa Najeriya’

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin a binciki dukkan kwangilolin kwantai ɗin ginin titina da ya gada, musamman waɗanda aka ce su na buƙatar ƙarin kuɗi a Ma’aikatar Ayyuka, domin tantance gaskiya, bin-diddigi da kuma ƙa’ida wajen ƙarasa ayyukan.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka, lokacin da yake wa manema labarai ƙarin bayani a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba.

Ya ce majalisar zartarwa ta yanke shawarar jingine ayyukan kwangilolin Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, waɗanda gwamnatin Tinubu ta gada, masamman waɗanda ke buƙatar sai an ƙara narka masu maƙudan kuɗaɗe.

Ya ce Shugaba Tinubu ya ce wannan takardar shawarar da Ministan Ayyuka, Davida Umahi ya gabatar wa Majalisar Zartaswa, ya na so a binciki kwangilolin kuma a sake tattauna batun su a taron Majalisar Zartaswa na gaba.

Idris ya ce za a yi bin-diddigin ne domin sake nazarin ayyukan da ke buƙatar ƙarin kuɗi da waɗanda ke buƙatar duba shi kacokan.

Minista Idris ya ce Tinubu ya umarci Ministan Ayyuka ya yi aiki tare da Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare da Ministan Harkokin Kuɗaɗe su sake nazarin ayyukan kwangilolin, domin gabatar da su a bisa tsarin ƙeƙe-da-ƙeƙe, wanda ke bisa turbar ƙa’idojin da ke cikin dokokin kasafin kuɗi.

Ministan ya ƙara da cewa, “duk inda ke buƙatar tilas sai an ƙara kuɗi, to za a gabatar da batun sa a taron Majalisar Zartaswa na gaba, domin a sake tattaunawa akai.

Idris ya ce Majalisar Zartaswa ta kuma tattauna dangane da Majalisar Tantance Kwangiloli (National Procurement Council), wadda kusan tsawon shekaru 17 kenan ta daina yin wani tasiri.

A kan haka ya ce Shugaban Ƙasa ya aika da ƙudiri a Majalisa, wanda tuni har an yi masa karatun farko.

“Maƙasudin yin haka shi ne domin mu tabbatar da Majalisar Tantance Kwangiloli mai tasiri, karsashi wadda za ta riƙa duba da nazarin kowace kwangila, domin tabbatar da sahihancin adadin kuɗaɗen da za a kashe mata,” inji ministan.

People are also reading