Home Back

Swiatek ta lashe French Open bayan doke Paolini

bbc.com 2024/7/7
Iga Swiatek

Asalin hoton, Getty Images

Iga Swiatek ta yi nasarar lashe French Open karo na uku a jere ranar Asabar, bayan da ta doke Jasmine Paolini.

Swiatek ƴar kasar Poland mai shekara 23, ta ci gaba da mamaye gasar ƙwallon tennis ta kan taɓo ta Roland Garros da cin 6-2 6-1.

Wannan shi ne kofi na hudu da ta lashe a birnin Paris, kuma Grand Slam na biyar, bayan lashe US Open a 2022.

Swiatek ta yi bajinta kamar yadda Monica Seles da Justine Henin suka yi a tarihin lashe kofin karo uku a jere tun bayan fara gasar mata a 1968.

Ita ce matashiyar da ta zama ƙwararriyar ƴar wasa ta kuma lashe Roland Garros hudu.

Bayan da ta yi nasarar ɗaukar kofin sama da awa ɗaya, Swiatek ta zuba gwiwa biyu kasa daga baya ta dunga rawa a cikin filin tennis.

Bajintar da Swiantek ta yi:

Swiatek ta yi nasarar cin wasa 21 a jere a French Open - ta zama ta hudu a yawan lashe wasannni tun bayan da aka aka fara gasar Open.

Swiatek ta yi nasarar lashe karawa 35 daga 37 a gasar ta Roland Garros

Ba ta yi rashin nasara ba a Paris tun daga 2021

Wadanda ke kan gaba a lashe kofin sun hada da Chris Evert mai bakwai da Steffi Graf mai shida da Justine Henin mai hudu sai kuma ƴar kasar Poland.

People are also reading