Home Back

SHEKARA ƊAYAR MULKIN TINUBU: ‘Najeriya ba ta aiki, Tinubu ne dai ke aikin-baban-giwa’ – Atiku

premiumtimesng.com 2024/6/26
Jami’ar Jihar Chicago ta mika bayanan karatun Tinubu ga Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ce Najeriya ba ta aiki a tsawon shekara ɗaya cur da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya shafe kan mulki, ‘sai dai Tinubu ɗin ne ke ta tafka ‘aikin-baban-giwa.’

Ya ce babu wani abin a zo a gani da Tinubu ya yi, sai shirme, kirdado da harankazamar da a kullum sai ƙara nutsar da ‘yan Najeriya cikin raɗaɗin tsadar rayuwa yake yi.

Ya ce tsare-tsaren tattalin arzikin da Tinubu ya bijiro da su duk babu alheri, tasiri ko alfanu a tattare da su, sai dai masifu da ƙuncin rayuwa.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Tinubu ya ce Tinubu ya shammaci ‘yan Najeriya sun ɗauka zai yi masu abin kirki, yayin da ya yi masu alƙawarin sake fasalin tattalin arzikin ƙasa, amma ba su sani ba ashe tubalin toka ne.

Sai dai Atiku ya ce babu wani alƙawarin da Tinubu ya cika tsawon watanni 12 da ya shafe kan mulki, sai ƙara jefa tattalin arzikin ƙasa cikin masifa.

“Taɓarɓarewar da tattalin arzikin Najeriya ya yi a cikin wannan shekara ɗaya, ba a ga irin haka ba a shekarun da suka gabata. Ga rashin aikin yi ya ƙaru, talauci da fatara sun ƙaru. an samu ƙaruwar miliyoyin marasa galihu. Najeriya wadda a baya ita ce mafi ƙarfin tattalin arziki a Afrika, yanzu ita ce ta 4. Ta na bayan Aljeriya, Masar da Afrika ta Kudu.

“Guyawun ‘yan Najeriya sun karye, babu komai a wannan gwamnatin sai tulin farfaganda, sai taɓarɓarewar tattalin arziki.”

People are also reading