Home Back

Hamas ta amince da tayin tsagaita wuta a Gaza

dw.com 2024/5/19
Gazastreifen | Flucht aus Rafah
Hoto: AFP/Getty Images

Masu aiko da rahotanni daga yankin sun ce jim kadan bayan sanar da wannan mataki da aka dade ana jira jama'a sun fastsama kan titunan birnin Rafah inda suka yi ta raye-raye na nuna murna har ma da harba bindiga a sarararin samaniya.

Karin bayani: Biden: Fata kan tsagaita wuta a Gaza

Wani jigo a kungiyar ta Hamas ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa yanzu zabi ya rage ga Isra'ila bayan da kungiyar ta bayyana cewa ta amince da tayin sulhun da kasashen Qatar da Masar da ke kai komo wajen shiga tsakani a rikicin gaza suka gabatar mata.