Home Back

Sin Na Fatan EU Za Ta Kiyaye Cinikayya Cikin ‘Yanci Tare Da Yin Watsi Da Ba Da Kariya

leadership.ng 2024/6/26
Sin Na Fatan EU Za Ta Kiyaye Cinikayya Cikin ‘Yanci Tare Da Yin Watsi Da Ba Da Kariya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Talata cewa, kasar Sin na fatan kungiyar tarayyar Turai EU za ta mutunta alkawarinta na tabbatar da yin cinikayya cikin ‘yanci da kuma yin adawa da ba da kariya ga cinikayya, da yin aiki tare da kasar Sin wajen kiyaye moriyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da EU. 

Mao ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai yayin da take mayar da martani kan kalaman da wani jami’in kungiyar ta EU ya yi, inda ya ce, yana da matukar wahala a “daina mu’amala” da kasar Sin, yana fatan ci gaba da dangantaka ta samun moriyar juna.

Mao ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje, da samar da yanayin kasuwanci mai kyau bisa gaskiya ga kamfanoni daga dukkan kasashen duniya.

Mao ta kara da cewa, a ko da yaushe kasar Sin na ganin cewa, manufar dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da EU, ita ce moriyar juna da samun nasara tare, kuma ba da kariya ga cinikayya ba ta da makoma, yayin da bude kofa ga kasashen waje da hadin gwiwa su ne hanya mafi dacewa. (Yahaya)

People are also reading