Home Back

Kula Da Fata Mai Maiko Da Ke Bata Kwalliya

leadership.ng 2024/4/29
Kula Da Fata Mai Maiko Da Ke Bata Kwalliya

Fata mai maiko kan ba wa wasu mata matsala musamman saboda yadda yake yawan bata musu kwalliya.

Mun kawo muku wasu hanyoyi da za ku yi amfani da su don kawo karshen wannan matsala taku:

 Na farko shi ne yawan rufe fuska ta hanyar amfani da kwai.

 Yadda ake yin amfani da kwai shi ne za ki fasa danyen kwai, ki cire kwanduwar ki bar farin.

 Sai ki lullube fuskarki da tishu sannan ki yi amfani da burushin shafa kayan kwalliya kina dangwalar ruwan kwan kina shafawa a tishun da ki ka lullube fuskarki da ita har sai ko’in a fuskarki ta jike da ruwan farin kwan.

 Ki bar shi na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan ki wanke da ruwan dumi.

 Hanya ta biyu ta magance maikon fuska ita ce yawan goge fuskarki da lemon zaki ko lemon tsami akalla na minti bakwai zuwa goma kafin shafa kayan kwalliya.

 Yin hakan na magance maikon fuska da kuma sanya laushi da shekin fata.

 A lura cewa idan aka yi wannan hadin to ba kya bukatar wanka da sabulu, amma za ki iya amfani da ruwan sanyi ko na dumi wajen dirje jikinki da kyau ta yadda kwabin zai wanku sosai.

 Na uku; Shi ne duk man shafawa ko ‘cream’ din da za ki yi amfani da shi ya zama an rubuta FOR OILY SKIN  wato na fata ne (Domin masu maikon fata) ko kuma FOR ALL SKIN TYPES (domin kowace irin fata) a jiki.

 Kar ki biye masa saboda dadin kamshinsa ko don shi ake yayi ko kuma tsadarsa.

 Wadannan abubuwan za su sa fatarki ta daina maiko kuma ko da kin yi kwalliya, babu ruwanki ballantana maikon fuska ya bata miki ita.

 
People are also reading