Tinubu Ya Nada Dan Arewa Shirgegen Mukami a Gwamnatinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Tanimu Yakubu a matsayin sabon darakta janar na ofishin kasafin kuɗi na tarayya.
Naɗin da shugaban ƙasan ya yiwa Tanimu Yakubu na zuwa ne bayan wa'adin Mista Ben Akabueze ya ƙare.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Tanimu Yakubu a matsayin darakta janar na ofishin kasafin kuɗi na tarayya, bayan ƙarewar wa'adin Mista Ben Akabueze."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Tanimu Yabuku ƙwararren masanin tattalin arziƙi ne wanda ya riƙe muƙamin babban mai bada shawara kan tattalin arziƙi ga tsohon shugaban ƙasa daga shekarar 2007 zuwa 2010, tsohon shugaban bankin FMBN daga shekarar 2003 zuwa 2007."
"Ya kuma taɓa riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi, tattalin arziƙi a jihar Katsina daga shekarar 1999 zuwa 2003."
- Ajuri Ngelale
Shugaba Tinubu ya godewa darakta janar mai barin gado, Ben Akabueze bisa aikin da ya yi tare da yi masa fatan nasara a dukkanin inda rayuwa ta kai shi nan gaba.
Asali: Legit.ng