Home Back

Kafa Kananan Rukunoni Ba Zai Haifar Da Komai Ba Face Tsananta Sabani

leadership.ng 5 days ago
Kafa Kananan Rukunoni Ba Zai Haifar Da Komai Ba Face Tsananta Sabani

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar ta yanar gizo ya nuna cewa, kashi 93.1 cikin kashi 100 na wadanda suka amsa tambayoyin, sun yi ammana cewa, ya kamata a samu tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik ta hanyar tattaunawar siyasa, inda suka bayyana adawa da yunkurin kafa NATO irin na Asiya.

Adadin mutanen da suka musu tambayoyin da ra’ayin da suka bayyana, tamkar amsa kuwwa ce ga ra’ayi da kiran da kullum Sin ke yi na a warware matsaloli da sabani ta hanyar tattaunawa. Ya kuma kara bayyana kyamar da galibin al’ummomin duniya ke yi da yake-yake da muradinsu na son zaman lafiya. Sai dai, wannan ra’ayi ya bambanta da na wasu ’yan tsiraru dake neman tada rikici ta kowanne hali.

Rikicin da har yanzu yake ci yake cinyewa tsakaninn Ukraine da Rasha, wani gargadi ne cewa, irin wannan yunkuri a yanayin da ake ciki yanzu a duniya, bai kamata ma ya taso ba, muddun ana son tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali, domin jefa duniya zai yi cikin karin tashin hankali.

Kafa kananan rukunonin kawance ko na taron dangi, ba zai haifar da komai ba face rarrabuwar kawuna da kara tsananta sabanin da ake fuskanta, maimakon yunkurin da ake yi na samar da fahimtar juna tsakanin mabambantan al’ummomin duniya da zummar samar da al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil adama.

Duniya ta sauya, kan kasashe ya waye, don haka babu wata kasa da za ta amince da babakere ko mulkin mallaka. Tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe ko wani yanki, ba zai haifar da da mai ido ba. Kasashen dake yankin Asiya da Pasifik, suna da kamanceceniya ta fuskar yanayin rayuwa da al’adu da muradu da sauransu. Haka kuma, su suka san gwagwarmayar da suka yi ta samun ’yanci da matsayin da suka kai a yanzu, don haka, babu wanda ya fi su sanin hanyar warware sabanin dake akwai tsakaninsu domin cimma zaman lafiya, kuma hanya daya tilo ita ce tattaunawa da tuntubar juna a siyasance. (Faeza Mustapha)

People are also reading