Al'ummar Jamhuriyar Nijar sun yi bikin Sallah Karama
Yau al’ummar Jamhuriyar Nijar suka gudanar da Sallah Karama bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal da mahukuntan kasar suka yi a jiya Litinin.
Wallafawa ranar: 09/04/2024 - 14:52
Bayanai sun ce mahukuntan na Nijar sun tabbatar da ganin jinjirin watan na Shawwal ne a jihohi akalla biyar da ke fadin kasar, abinda ya sanya suka bayyana wannan Talata 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar Sallah wadda tayi daidai da 1 ga watan Shawwal shekara ta 1445.
A yayin da Nijar ke bikin kammala Azumin watan Ramadana, akasarin kasashen Musulmi sun bayyana Laraba ne a matsayin ranar Sallar karama saboda rashin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin.
Daga cikin kasashen da suka cika kwanaki 30 a watan na Ramadana akwai Saudiya, Yemen, Syria, Masar, Iraqi, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Lebanon, da Yankin Falasdinu da kuma Najeriya.