Home Back

Copa America: Argentina, Canada Sun je Wasan Gab da Kusa da na Ƙarshe

premiumtimesng.com 3 days ago
Copa America: Argentina, Canada Sun je Wasan Gab da Kusa da na Ƙarshe

Tawagar ƙasashen Argentina da Canada dake buga gasar cin kofin kasashen kudancin Amurka sun samu nasara tsallakawa zuwa wasan gab da kusa da na karshe a rukunin A.

Argentina ta samu wannan nasara ne bayan doke kasar Peru 2-0 a wasan karshe na rukunin A da suka buga a daren jiya, inda ɗan wasan gaban tawagar Lautaro Martinez ya tura ƙwallaye biyu, ta farko a mintina na 47 sai ta biyu mintina 86.

Yanzu haka dai Lautaro Martinez ne yafi kowa yawan zura kwallaye a gasar, inda ya zura huɗu a raga jumilla, bayan ya zurawa Chile 1, Canada 1 sai kuma Peru 2.

Argentina dai ta ƙare wasannin rukuni da maki 9 bayan buga wasanni 3 ba tare da an zura mata kwallo ko ɗaya ba.

Canada kuwa ta samu nasarar tsallakawar ne a farko a tarihin ta, bayan buga kunnen doki 0-0 da Chile a daren jita Lahadi, tare da haɗa maki hudi jumulla.

Kawo yanzu dai mai rike da kofin Argentina ta ƙare a mataki na ɗaya da maki 9, Canada ta biyu da maki 4, Chile ta uku da maki 2 sai kuma ta karshe Peru da maki 1.

A daren yau za a barje gumi a wasannin karshe na rukunin B tsakanin Mexico da Ecuador sai Jamaica da Venezuela da ƙarfe 1 na dare.

Argentina ta samu nasara a wasanta da Peru ba tare Lionel Messi ba, saboda ɗan wasan bai gama murmurewa daga karamin raunin da ya samu ba.

People are also reading