Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Daren Sallah, Sun Kashe Mutane, Sun Sace Wasu A Sokoto
Hasashen gudanar da bukukuwan murnar Sallah Eid-el-Kabir a unguwar Dukun Doki da ke ƙaramar hukumar Gwadabawa a jihar Sakkwato ya koma ban tausayi yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari inda suka kashe mutane shida tare da yin awon gaba da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba sa’o’i kadan kafin bikin.
Harin dai ya faru ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Asabar, lamarin da ya haifar da firgici a yayin da maharan ɗauke da makamai suka yi ta harbi ba kakkautawa, lamarin da ya tilastawa mazauna ƙauyuka da dama tserewa cikin daji da kuma yankunan da ke kusa da su domin tsira da rayukansu.
Wani mutum a ƙauyan mai suna Bala Tudun Doki ya bayyana cewa harin bazatan ya haifar da fargaba a ƙauyuka da dama da suka hada da Asara Kudu, da Asara Arewa, da Chimola Arewa, da Chiomola Kudu, Gidan Kaya, da Gigane, da Salame, da kuma Mammande, har yanzu ba a san ainihin adadin mutanen da aka sace ba, domin har yanzu ba a san ko su waye suka nemi mafaka a wurare masu tsaro.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da mutuwar mutane da kuma rashin tabbas da ake ci gaba da yi dangane da adadin mutanen da aka sace. Ya ce, “An tabbatar da mutuwar mutane shida a asibitin, amma har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba, zan sanar da ku da wani karin bayani.”
Karamar Hukumar Gwadabawa da ke shiyyar Sakkwato ta Gabas ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a tsawon shekaru, lamarin da ya ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin.