Kwale Kwale Ya Kife da Masu Tserewa Harin 'Yan Bindiga a Neja, Mutum 4 Sun Rasu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Wani kwale-kwale da ke ɗauke da wasu mazauna ƙauyukan da ke tserewa hare-haren ƴan bindiga a jihar Neja ya kife.
Mutanen dai sun fito ne daga ƙauyen Gurmana da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa bayan kifewar kwale-kwalen, mutum huɗu sun rasa rayukansu.
Mutanen ƙauyen sun gudu zuwa wani tsibiri ne domin buya daga ƴan bindiga a daren ranar Laraba bayan ƴan bindigan sun kawo hari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kifewar kwale-kwalen ta auku ne a ranar Alhamis lokacin da suke dawowa bayan da ƴan bindigan suka gama kai farmaki a ƙauyukan.
An tattaro cewa mutanen ƙauyen suna zuwa tsibirin ne da ke tsakiyar kogin Kaduna domin ɓuya daga ƴan bindigan waɗanda suke jin tsoron kogin.
Ƴan bindigan sun kashe mutum uku a hare-haren na daren jiya, sannan sun sace shanu masu yawa tare da yin awon gaba da mutane da dama a Bassa kusa da Gurmana.
Asali: Legit.ng