Home Back

"Bana Son Zama Ubangida" Malam El-Rufa'i Ya Mayar da Martani Kan Abin da Ke Faruwa a Kaduna

legit.ng 2024/5/19
  • Mallam Nasiru El-Rufai ya mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa a jihar Ƙaduna karkashin mulkin Uba Sani
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sau 5 kaɗai ya je Kaduna tun bayan sauka mulki saboda ba ya som tsoma baƙi a gwamnatin Uba Sani
  • Wannan kalamai na Mallam Nasiru na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani ya koka kan tulin bashin da ya gada daga gwamnatin da ta gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ya ce baya son a kira shi ubangida a jihar Kaduna.

Wannan kalamai na El-Rufai na zuwa bayan gwamnan Kaduna, Malam Uɓa Sani, ya koka kan tulin bashin da ya gada daga tsohon gwamnan, rahoton Daily Trust.

Nasiru Ahmad El-Rufai.
Mallam El-Rufai ya ce ba ya da burin zama ubangida a jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai Asali: Facebook

Da yake jawabi a wurin wani taro da aka gayyace shi a jihar Borno ranar Litinin, Malam El-Rufai ya ce sau 5 kacal ya je Kaduna tun da ya sauka daga mulki shekara guda kenan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasu kalamai da ake kallo tamkar martani ne ga rikicin da ke neman kunno kai a siyasar Kaduna, tsohon gwamnan ya ce ba ya tsoma baki a harkokin mulkin Uba Sani.

“Ba na son zama ubangida, shi ya sa ba na tsoma baki a al'amuran da ke faruwa a jihar Kaduna, ina son shi (gwamna) ya koya da kansa kuma ya tafiyar da mulki da kansa.
"Abin da muka rasa shi ne shugabanci na gari kuma ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo jagoranci na gari shi ne shugaba ya samu mutanen kirki a kusa da shi domin sauke nauyin da ke kansa.
"Allah ne kaɗai ke da karfin ikon tafiyar da komai da kansa, amma duk da yadda shugaba ya kai ga zama nagari zai yi tasiri ne daidai gwargwadon mutanen da ke kewaye da shi.
"Shiyasa masu iya magana ke cewa ingancin kowace ƙasa na tattare ne da nagartar ma'aikatanta."

- Malam Nasiru El-Rufai.

Asali: Legit.ng

People are also reading