Home Back

Yadda Kasar Sin Ke Samar Da Gudummawa Ga Tabbatar Da Bunkasuwar Duniya Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

leadership.ng 2024/5/19
Yadda Kasar Sin Ke Samar Da Gudummawa Ga Tabbatar Da Bunkasuwar Duniya Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

Kwanan nan, an gudanar da taron kasa da kasa kan makamashi karo na 26 a birnin Rotterdam na kasar Netherlands. Taken taron shi ne “A sake tsara fasalin makamashi ga dan Adam da duniya”, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar kalubale na sake fasalin makamashin da ake amfani da su, taron ya jawo wakilai kusan dubu 20 daga sassan makamashi na duniya. Amin Nasser, babban darektan kamfanin Saudi Aramco mai samar da man fetur na kasar Saudiyya, ya yaba da gudummawar da kasar Sin ta samar ta fannin cimma burin samun daidaito tsakanin yawan hayaki mai dumama yanayi da za a fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin a fadin duniya. A cewarsa, ta hanyar rage kudin sarrafa farantan samar da wutar lantarki ta hasken rana, kasar Sin ta tallafa wa kasashen duniya, ciki har da kasashen yamma, wajen bunkasa sabbin makamashi, kuma abin haka yake ta fannin motoci masu aiki da lantarki. 

A lokacin da kasar Amurka ke ta zargin kasar Sin da cewa wai “ta wuce misali wajen samar da sabbin makamashi”, furucin na malam Amin Nasser ya jawo hankalin kasa da kasa, ba kawai sabo da matsayinsa da na kamfaninsa ta fannin makamashin duniya ba, har da ma adalci da ya yi kan rawar da kasar Sin ke takawa wajen samar da makamashi mai tsabta, da ma rage fitar da iskar Carbon.

A halin da ake ciki na kara samun zafin yanayi, da ma bala’u daga indallahi, yana ta kara zama dole a sake fasalin makamashi da ake amfani da su. Duk da haka, aikin ba shi da sauki. Don tabbatar da daidaiton kasa da kasa na tinkarar sauyin yanayin duniya, a cikin ‘yan shekarun baya, kasar Sin ta dogara ga kirkire-kirkiren fasahohi, da manyan kasuwanninta, da cikakken tsarin masana’antunta, kuma ta yi ta samun ci gaba ta fannin sabbin makamashi. Ban da biyan bukatun cikin gida, kayayyaki masu nasaba da sabbin makamashi da kasar Sin ta samar sun kuma samar da dama ga kasashen duniya, musamman ma kasashen Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa, wajen sauya makamashin da suke amfani da su da ma tabbatar da dauwamammen ci gabansu.

In mun duba kasashen Afirka, bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, da ma tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kasar Sin ta aiwatar da shirye-shirye daruruwa na samar da wutar lantarki ta makamashi masu tsabta. A kasar Kenya, tashar samar da wutar lantarki da makamashin rana ta Garissa, wadda wani kamfanin kasar Sin ne ya gina, ta kasance mafi girma a gabashin Afirka, kuma bayan da aka fara aiki da ita a shekarar 2019, ta rika samar da wuta sama da KW miliyan 76 a kowace shekara, wadda ke iya biyan bukatun mutane sama da dubu 380, kana ta yi matukar saukaka matsalar karancin wutar lantarki da aka fuskanta a wurin. Sai kuma a Nijeriya, a watan Mayun bara, an fara aiki da bas-bas masu aiki da lantarki da kamfanin samar da bas-bas na kasar Sin ya samar, matakin da ke da matukar ma’ana ga tabbatar da dauwamammen ci gaban harkokin zirga-zirga, da ma sake fasalin makamashi a kasar da ma shiyyar yammacin Afirka baki daya. A ganin Adhere Cavince, masanin ilmin huldar kasa da kasa na kasar Kenya, kasar Sin ba kawai tana kokarin sauya makamashin da take amfani da su ba, har kullum tana kuma hada kai da kasashen Afirka, har ma ta zama babbar abokiyar hadin gwiwa ga kasashen Afirka, wajen bunkasa makamashin da ake samarwa ta hasken rana da kuma karfin iska.

Ya zuwa bara, shekaru 10 a jere ke nan kasar Sin tana kan matsayi na farko a duniya, wajen samar da wutar lantarki da sabbin makamashi. Ban da haka, kasar Sin ta kuma samar da kaso 50% na na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska, da kuma kaso 80% na na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana da ake bukata a duniya. A cikin shekaru 10 da suka wuce, matsakaicin kudin da ake bukata wajen samar da wutar lantarki ta karfin iska da ta hasken rana, ya ragu da kashi 60% da kuma 80% kowanensu, kuma hakan ba ya rasa nasaba da babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar. A wata makala da kafar Bloomburg ta fitar, an ce, kayayyaki masu nasaba da sabbin makamashi da kasar Sin ta samar cikin farashi mai sauki, sun samar da damar sauya fasalin makamashin duniya.

Amma duk da haka, ko ta fannin cimma burin da aka saka a yarjejeniyar Paris, ko kuma ta cimma burin kasar Sin na kaiwa kololuwar fitar da iskar Carbon zuwa shekarar 2030, da kuma kawar da illar sa zuwa shekarar 2060, ba a kai ga biyan bukatun ba bisa karfin kasar Sin ta fannin sabbin makamashi. Hukumar makamashi ta duniya (IEA) ta yi gargadin cewa, har yanzu ana yawan amfani da makamashi irinsu kwal, da mai da iskar gas, don haka ma, kalubalen da ake fuskanta ba wai na “ana samar da makamashi mai tsabta fiye da kima ba” ne, sai ma dai matsalar karancinsu.

Amurka ta na son shawo kan masana’antun samar da kayayyaki masu nasaba da sabbin makamashi na kasar Sin ne don kare masana’antun ta, amma hakan na dakile kokarin da sassan kasa da kasa ke yi na sake fasalin makamashin da ake amfani da su, tare da lalata moriyar kasashe masu tasowa, ta fannin tabbatar da dauwamammen ci gabansu.

A hakika, cikin jirgi guda ne daukacin ‘yan Adam suke, kuma ba za a kai ga tinkarar kalubalen sauyin yanayi da suke fuskanta ba, har sai sun hada gwiwa da juna. (Lubabatu Lei)

People are also reading