Home Back

Ana binciken Lamuwa, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje da ƙoƙarin neman haɗin kan matar auren da ke aiki ƙarƙashin sa

premiumtimesng.com 2024/6/26
Ana binciken Lamuwa, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje da ƙoƙarin neman haɗin kan matar auren da ke aiki ƙarƙashin sa

Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya aika wa Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje, Ibrahim Lamuwa, wasiƙar tuhuma, bisa ƙorafin zargin Ana zargin neman haɗin kan matar auren da ke aiki ƙarƙashin sa.

Lamuwa wanda ya yi Jakadan Sanagal da Mauritaniya a lokaci guda, kafin naɗa shi Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje.

Wata mata ce mai suna Simisola Fajemirokun-Ajayi, hadimar Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ce ta yi ƙorafi kan Lamuwa.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Minista Tuggar ya aika wa Shugaban Ma’aikata takardar ƙorafin da matar ta yi, domin a yi bincike.

Yayin da Minista shi ne babba a ma’aikata, shi kuma Babban Sakatare ke kula da duk ayyukan yau da kullum.

Mohammed Ahmed, Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Shugaban Ma’aikata, ya tabbatar da cewa an aika wa Lamuwa takardar tuhumar sa neman jin ba’asi.

Ya ce an aika masa takardar neman jin ta bakin sa ne domin a yi masa adalci, ta hanyar jin ta bakin sa.

“Daga amsar da ya bayar za a ɗauki mataki na gaba.” Ya ƙara da cewa za a yi bincike sosai domin a ba mai gaskiya gaskiyar sa.

‘Ƙarya da sharri ta ke min, ban taɓa neman kusantuwa da ita ba’ – Lamuwa:

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Lamuwa ya ƙaryata zargin da matar ta yi masa, a cikin wata amsa da ya bayar.

A cikin amsar da ya aika Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, ya ce an ƙirƙiro sharri ne an saƙala masa, ta ce ya yi yi ƙoƙarin neman haɗin kan kusantuwa da ita.

Ya ce ta yi masa sharri ne saboda ya sha ƙin amincewa da buƙatar kuɗaɗen da matar ke yawan yi daga ma’aikatar ba bisa ƙa’ida ba.

Daga cikin zargin da ta yi wa Lamuwa, har da umarnin da ya taɓa bata cewa ta je ta same shi a wani otal da ya kama.

People are also reading