Home Back

Tarihi Ya Maimaita Kansa: Yadda Aka Fara Raba Masarautu da Rusa Su a Jihar Kano

legit.ng 2024/9/27
  • A tarihin jihar Kano an samu sabani tsakanin masu sarautar gargajiya da shugabannin gwamantin jihar da dama a lokuta daban-daban
  • Hakan ya yi sanadiyyar sauke wasu sarakunan, a wasu lokutan kuma har ya kai ga kara yawan masarautun jihar domin manufar siyasa
  • A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku yadda rikicin siyasa ya jawo rusa masarautun jihar Kano da kara yawansu a shekarun baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A ranar 22 ga watan Oktoban shekarar 1963 aka naɗa marigayi mai martaba Ado Bayero sarautar Kano.

Masarautar kano
Yadda aka ragewa Ado Bayero karfi ta hanyar kirkiro masarautu a Kano. Hoto: Antonio Ribeiro|Pious Utomi Ekpei Asali: Getty Images

Ado Bayero ya cigaba da mulki lafiya har bayan zaben shekarar 1979 da ya ba Abubakar Rimi damar zama gwamnan Kano inda suka fara samun sabani, rahoton Daily Trust.

Sabanin da aka samu tsakanin gwamnatin Rimi da Ado Bayero har ya kai ga yin zanga-zanga a watan Yunin shekarar 1981.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar Rimi ya kara masarautun Kano

Bayan rikici ya yi ƙamari tsakanin Rimi da Ado Bayero, sai gwamnati ta kirkiro masarautu domin rage karfin mulkin mai martaba Ado Bayero, rahoton Channels Television.

A lokacin, Rimi ya kirkiro masarautun Gaya, Rano, Dutse da Auyo kuma ya ba su matsayi daya da Ado Bayero.

Bayan haka, Rimi ya kara daga darajar masarautun Kazaure, Gumel da Hadeja suka dawo suna kafada da kafada da sarautar Ado Bayero.

Ana cikin haka ne kuma sai Abubakar Rimi ya dawo da tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi I Wudil daga Azare a shekarar 1982 yana kokarin dawo da shi mulki amma hakan bai samu ba.

Sabo Bakinzuwo ya rusa masarautun Kano

A lokacin da aka yi zaben shekarar 1983, Aliyu Sabo Bakinzuwo ya kayar da Abubakar Rimi wanda hakan ya ba shi damar zama gwamnan Kano na wancan lokacin.

Ana rantsar da Sabo Bakinzuwo abin da ya fara shine rusa masarautun da Abubakar Rimi ya kirkiro da rage darajar wadanda ya ɗaukaka.

Kotu ta hana dawo da Sanusi II

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar rushe majalisar masarautar Kano.

Mai shari’a Mohammed Liman ne ya yanke hukuncin a kan bukatar da wani basarake, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar.

Asali: Legit.ng

People are also reading