Home Back

Karkatar Da Goron Sallah: Ku Dawo Da Kuɗin Ma’aikata Ko Mu Hukunta Ku” – Gwamnan Sakkwato

leadership.ng 2024/7/15
Karkatar Da Goron Sallah: Ku Dawo Da Kuɗin Ma’aikata Ko Mu Hukunta Ku” – Gwamnan Sakkwato

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya umurci jami’an ƙananan hukumomi da hukumomin ilimi a ƙananan hukumomi da su gaggauta dawo da dubu 30 kuɗin goron Sallah da suka karkatar waɗanda gwamnati ta ba wa ma’aikata kyauta ko su fuskanci hukunci. 

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a fadar gwamnati a yayin da yake jawabi ga jama’ar da suka zo yi masa barka da kammala aikin Hajji lafiya. Ya nuna damuwa kan halayyar da wasu jami’an kuɗi suka nuna musamman a matakin ƙananan hukumomi waɗanda suka hana ma’aikatansu kuɗin goron sallar.

Ma’aikatan ƙananan hukumomi da dama sun yi ƙorafin ba su samu kuɗin ba kamar yadda gwamna ya bayar da umurni, wasu sun ce an biya su dubu 20 bayan sallah maimakon dubu 30, wasu kuma ba su samu kuɗin ba bakidaya.

Ya ce “Na yi mamakin yadda wani zai hana ma’aikatan tallafin da muka ba su domin su samu sukunin gudanar da hidimar Sallah babba cikin tsanaki.”

“Ya zama dole waɗanda suka karkatar da kuɗin su dawo da su da gaggawa ko kuma mu ɗauki kwakkwaran matakin ladabtar da su.” Gwamnan ya bayyana.

Ya ƙara da cewa za su tabbatar waɗanda suka aikata laifin sun girbi abin da suka shuka domin ya zama darasi ga na baya.

Haka ma ya buƙaci shugabannin hukumomin da aka aikata irin wannan badaƙalar da su gaggauta tattara bayanan dukkanin ma’aikatan da lamarin ya shafa, su kuma tabbatar an dawo masu da haƙƙinsu.

People are also reading