Home Back

‘Mun janye umarnin dakatar da ƙarin kuɗin wutar lantarki, tunda maganar ta na kotu’ – Majalisar Dattawa

premiumtimesng.com 2024/6/16
SAKA SAKAMAKON ZABE A YANAR GIZO: An kicime a majalisar Dattawa

Majalisar Dattawa ta bayyana janye umarnin dakatar da ƙarin kuɗin wutar lantarki wanda ta bayar kwanan baya.

Majalisar ta janye umarnin hana ƙarin kuɗin ne, bayan wani kwamiti da ta kafa ya bada shawarar ta janye umarnin, domin a yanzu maganar ƙarin kuɗin ta na kotu.

Idan ba a manta ba, Majalisar Dattawa ta yanke shawarar cewa a dakatar da ƙarin kuɗin wuta wanda Hukumar Wutar Lantarki ta NERC ta bayar da sanarwar yi.

Daga baya kuma ta naɗa kwamiti domin bin ba’asin batun ƙarin kuɗin wutar.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai lura da Harkokin Kasuwanci, Sanata Titus Zam ne ya bayar da shawarar a janye umarnin, domin rigimar ta na kotu a halin yanzu.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya bayyana sanarwar janye umarnin kada a yi ƙarin kuɗin wutar lantarkin bayan mafiya yawan dattawan sun nemi a janye umarnin.

Cikin watan Fabrairu ne Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki, kuma ta umarci Kwamitin Harkokin Makamashi ya binciki dalilin yin ƙarin.

Duk da wannan ƙin amincewa da Majalisar Dattawa ta yi, hukumar wutar lantarki wato NERC ta bayyana ƙarin kuɗin a cikin watan Afrilu, inda masu samun wuta ƙarƙashin rukunin Band A a ka yi masu ƙari daga Naira 68 kowane kilowatt na tsawon awa ɗaya zuwa Naira 225.

Yayin da Kwamitin Makamashi ƙarƙashin Sanata Enyinnaya Abaribe ya damƙa wa Majalisar Dattawa rahoton sa, sai yawancin dattawan suka ce tunda maganar ta na kotu, ya fi kyau majalisa ta janye umarnin rashin amincewa da ƙarin kawai, a ƙyale kotu ta yi hukunci.

Tuni dai aka maka Gwamnatin Najeriya kotu, ana ƙalubalantar ƙarin kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da raɗaɗin tsadar rayuwa ke ƙara nukurkusar zukatan ‘yan Najeriya.

People are also reading