Home Back

Gwamnatin Tinubu za ta binciki sake duba yadda gwamnatin Buhari ta jinginar da filayen jiragen sama biyu – Minista Keyamo

premiumtimesng.com 2024/7/1
CANJIN TAKARDUN KUƊI: Allah Sarki Shugaba Buhari, ga abinda ya hangowa wa Arewa – Daga Baba Habu Fagge

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za a sake bibiyar kwangilar jinginar da Filayen jiragen sama guda biyu, wanda gwamnatin Buhari ta yi.

Keyamo ya bayyana haka a Abuja, a taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa.

“Za mu sake ko sabunta kwangilar jinginar da filayen jiragen biyu, domin a fito da komai a yi komai keƙe-da-ƙeƙe.

Ya ce har yanzu haka an dakatar da batun kafa Nigerian Air.

Ya ƙara da cewa Jirgin Kamfanin Ethiopian Airlines ne tsohon Ministan Hadi Sirika ya shafa wa fenti da tutar Najeriya, ya ƙaddamar da shi.

“Tilas Nigerian Air ya zama na cikin gida kacokan”, inji Keyamo.

Cikin shekarar da ta gabata ne tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya yi gidogar ƙaddamar da Nigerian Air, Kwanaki biyu kafin ya sauka daga minista.

Kwanan nan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin sa da na ‘yar sa, bayan an damƙe shi ana neman Naira biliyan kusan 20 a hannun sa.

People are also reading