Home Back

Farashin Abinci Zai Faɗi Warwas Nan Da Kwanaki 180 – Ministan Noma

leadership.ng 2024/8/24
Farashin Abinci Zai Faɗi Warwas Nan Da Kwanaki 180 – Ministan Noma

Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa farashin kayan abinci a fadin kasar nan zai fadi warwas cikin kwanaki 180 (watanni 6).

Ministan ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta inda ya kuma bayyana wasu tsare-tsare da gwamnatin Tinubu ke yi domin cimma wannan aniyar.

Kyari ya bayyana dakatar da haraji kan shigo da kayayyakin abinci da suka hada da shinkafa da alkama da masara da wake. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin shigo da tan 250,000 na alkama da kuma tan 250,000 na masara wanda za’a rabawa masu kananan sana’o’i da masu sarrafawa a matsayin tsare-tsaren da za su sanya farashin kayayyakin ya fadi warwas a fadin kasar nan.

“Gwamnatinmu ta kaddamar da wasu tsare-tsare da nufin magance tsadar kayan abinci da ke addabar al’ummarmu a halin yanzu. Za a aiwatar da waɗannan matakan a cikin kwanaki 180 masu zuwa.

“Tsare-tsaren sun hada da bayar da damar shigo da kayayyakin abinci ba tare da haraji ba na kwanaki 150 ta kan iyakokin kasa da ruwa. Wadannan kayayyaki sun hada da masara, shinkafa, alkama, da wake,” in ji ministan.

Kayayyakin abincin da aka shigo da su za a sanya su ga kayyadadden farashin kasuwa (RRP).

People are also reading