Home Back

BIDIYO: HAJJIN BANA: An yi taron shuka itatuwa a filin Mina domin samar da inuwa lokacin aikin Hajji

premiumtimesng.com 2024/7/1
BIDIYO: HAJJIN BANA: An yi taron shuka itatuwa a filin Mina domin samar da inuwa lokacin aikin Hajji

A ranar Alhamis ne shugaban hukumar alhazai na Kasa, Jalal Arabi wanda Kodinatan Hukumar a Makka, Aliyu Tanko ya wakilta suka yi taron shuka itatuwa a filin Mina.

Wannan aiki da aka yi ya samu wakilcin wasu daga cikin jami’an gwamnatin Saudi da kuma na kungiyar PCAS, wacce tare ne aka gudanar da wannan aiki.

An shuka akalla itatuwa 20 da kuma Filawa wato furanni har 20,000 a Mina zuwa mahaɗar Muzdalifa.

Ranar Juma’a ce 1 ga Dhul-Hijja, wanda ke nuni cewa za a yi hawan Arafat ranar Asabar 15 ga Yuni sannan kuma ayi babbar Sallah ranar 16 ga Yuni kamar yadda mahukunta a Saudiya suka sanar.

Zuwa yanzu NAHCON ta kwashe Alhazai sama da 45,000 zuwa ƙasa mai tsarki a shirin fara aikin Hajji gadan-gadan wanda zai kankama a cikin mako mai zuwa.

People are also reading