Home Back

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Magana Bayan an Zarge Ta da Kisan Fararen Hula

legit.ng 2024/7/3
  • Rundunar sojin Najeriya ta yi martani ga shugaban ƴan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biyafara a kudu maso gabas
  • Shugaban kungiyar, Simon Ekpa ya zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla ga 'yan ƙabilar Ibo a kudu maso gabashin Najeriya
  • Sai dai rundunar sojin ta ware zare da abawa kan hakikanin abin da ya faru cikin wani sako da jami'in yaɗa labaran ta ya wallafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Rundunar sojin Najeriya ta yi bayani kan zargin kisan gilla ga yan ƙabilar Ibo a kudu maso gabashin Najeriya.

Shugaban kungiyar ƴan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biyafara, Simon Ekpa ne ya zargi rundunar soji da kisan.

Sojojin Najeriya
Rundunar soji ta musa kisan 'yan kabilar Ibo. Hoto: HQ Nigerian Army Asali: Facebook

Rundunar sojin ta wallafa sako a shafin ta na Facebook tana cewa Simon Ekpa na son tayar da fitina ne kawai amma ba ƙamshin gaskiya a cikin zancen sa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi sojoji da kisan farar hula

Simon Ekpa ya fito a wani bidiyo yana nuna sojojin Najeriya na kisan ƙare dangi ga 'yan ƙabilar Igbo a kudu maso yamma.

Ekpa ya yi ikirarin cewa sojin suna kashe Ibo a bakin kogi sannan su jefa gawar su a cikin ruwa saboda kada ma a samu gawa daga baya.

Rundunar soji ta musa kisan farar hula

Sai dai rundunar sojin ta mayar wa ɗan ta'addan martani bayan zurfafa bincike tana mai cewa mutanen da suke cikin bidiyon ba jami'an sojin Najeriya ba ne.

Ta kuma kara da cewa bincike ya tabbatar da cewa an dauki bidiyon a kudu maso yammacin Najeriya ne ba yankin da ɗan ta'addan ke magana a kai ba.

Sojoji: ba sauki ga 'yan ta'adda

Rundunar sojin ta ce ba gudu ba ja da baya kan yaƙi da ta'addanci musamman waɗannda suke neman lalata yankin kudu maso gabas.

Har ila yau rundunar ta mika sokon godiya ga 'yan ƙabilar Ibo da suka cigaba da goyon bayan rundunar sojin duk da farfaganda da ƴan ta'adda irinsu Simon Ekpa ke yaɗawa.

Sheikh Guruntum yana lafiya

A wani rahoton, kun ji cewa babban malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya Musa labarin cewa ya rasu.

Sheikh Guruntum ya bayyana haka ne yayin da mutane suka fara yaɗa jita jitar cewa ya yi mummunan hatsarin mota a jiya Laraba.

Asali: Legit.ng

People are also reading