Ana Tsaka da Rigimar Kano, Rikici Ya Kaure Tsakanin Masu Nadin Sarki a Wata Jiha
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Rikici ya barke tsakanin masu nadin sarki a kauyen Ifon da ke karamar hukumar Ose a jihar Ondo.
Hakan ya biyo bayan rarrabuwar kawuna tsakanin masu nadin sauratar kan wanda ya kamata a nada sarki a yankin.
Wani tsagi na masu nadin sarki sun zargi kokarin tilasta musu Prince Adelanke Odogiyon a matsayin Sarki, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun zargi wasu daga mukarraban gwamnati da neman kakaba musu Odogiyon domin biyan buƙatar kansu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren masu nadin Sarkin, Kehinde Falowo ya fitar a ya Alhamis 27 ga watan Yunin 2024.
A wani labarin, kun ji cewa wata Babbar Kotun jihar Ondo da ke zama a Akure ta rusa dokar da marigayi Oluwarotimi Akeredolu ya zartar na kirkirar karin kananan hukumomi 33.
Alkalin kotun Mai Shari'a, Adegboyega Adebusoye ya yanke wannan hukuncin a ranar Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 da muke ciki.
Adegboyega Adebusoye ya ayyana kirkirar kananan hukumomin a matsayin abin da ya sabawa kundin tsarin mulki kuma ya sabawa ka’ida.
Asali: Legit.ng