Home Back

Sojojin China sun hana gangamin tunawa da kisan Tiananmen

rfi.fr 2024/7/7
Tankokin yaƙin China a wurin da aka yi wa masu bore kisan gilla a Tiananmen a ranar 4 ga watan Yunin shekarar 1989
Tankokin yaƙin China a wurin da aka yi wa masu bore kisan gilla a Tiananmen a ranar 4 ga watan Yunin shekarar 1989 AP - Jeff Widener

Jami’an tsaro sun takura wa masu gudanar da gangamin tunawa da kisan gillar da aka yi wa wasu da ke bore a dandalin Tiananmen na ƙasar China shekaru 35 da suka gabata, yayin da aka cafke mutane a Hong Kong da suka fito don tunawa da wannan rana a  yau.

A rana irin ta yau ce, wato 4 ga watan shekarar 1989, tankokin yaƙin sojin China suka kutsa kai cikin dandalin na Tiananmen da zummar kawo ƙarshen wata zanga-zangar da ɗalibai da ma’aikata suka shafe tsawon makwanni bakwai suna gudanarwa a wancan lokaci don nuna goyon bayansu ga tsarin dimokuraɗiyya.

Bayan gwanman shekaru da murkushewar da sojoji suka yi wa masu boren, har yanzu  akwai tazara mai yawa tsakanin burin masu zanga-zangar da kuma tabbatar da ƴancin faɗin albarkacian baki, kuma wannan lamarin da ya faru a ranar 4 ga watan na Yuni, na ci gaba da zama abin kyama a China kamar yadda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ke cewa.

Kodayake gwamnatin China ta wancan lokacin ƙarkashin jam’iyyar Kwamunisanci, ba ta fitar da alƙaluman mutanen da aka yi wa kisan gillar ba a wancan lokacin, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da shaidun gani da ido sun ce, dubban mutane aka kashe.

Shugaban Taiwan Lai Ching-te ya ce, tunanin alhinin abin da ya faru a ranar 4 ga watan Yunin, ba za a taɓa iya goge shi ba  a kundin tarihi.

Gwamnatin Beijing dai ta fito ƙarara ta nuna adawarta ga duk wanda ya aibata China, tare da fakewa da lamarin yana yi mata katsalandar a harkokinta na cikin gida.

People are also reading