Home Back

An mayar da Aung San Suu Kyi daurin talala

dw.com 2024/5/19

A wannan Laraba gwamnatin mulkin sojan kasar Myanmar, ta mayar da tsoguwar jagorar gwamnatin farar hular kasar Aung San Suu Kyi daga gidan fursuna zuwa daurin talala a gidanta bisa dalilai na lafiya saboda tsananin zafi da ake fuskanta. Har ila yau gwamnatin ta yi ahuwa ga kimanin fursunoni 3,000. Mai magana da yawun gwamnatin sojan kasar ya tabbatar da labarin.

Aung San Suu Kyi da tsohon shugaban kasar da aka kifar Win Myint a shekara ta 2021 suna cikin wadanda aka mayar da su gida daurin talala. Ita dai Aung San Suu Kyi ficecciyar siyasa da ta yi suna a kasar ta Myanmar mai shekaru 78 da haihuwa tana zaman daurin shekaru 27 na laifukan da sojojin da suka yi juyin mulki suka tuhume ta da su daga cikin hanci da rashawa zuwa taka ka'idar annobar cutar corona.

Gwamnatin mulkin sojan ta dauki matakin sassaucin da sakin dubban fursunonin albarkacin bukukuwan sabuwar shekara ta kasar.

People are also reading