Home Back

Wata mata ta tayar da hayaniya ana tsaka da shari’a a kotu

dalafmkano.com 4 days ago

Kotun majistret mai lamba 51 karkashin mai Shari’a Hajara safiyo Usman, ta aike da wata mata asibitin kwakwalwa na Dawanau dan a binciki lafiyar ƙwaƙwalwar ta.

Tunda farko wani mutum ne mai sauna Ibrahim Muhammad, ya shigar da ƙara bisa yadda ya yi zargin cewar, matar ta doke shi da wani ƙarfe dan kawai ya tashe ta daga gidan da take haya.

Mai ƙarar ya bayyana cewar, kotu mai lamba 23 ta tashi matar daga gidan amma sai ta ɓalle ƙofar gidan ta sake dawowa gidan, ko da yaje dan jin dalili sai ta bubbuga masa wani ƙarfe.

Yayin da ake karanta mata ƙunshin tuhumar matar ta tayar da hayaniya a gaban kotun, har ma ta bayyanawa mai Shari’a cewar, duk wanda ya koma gidanta da niyar fitar mata da kaya kwanansa ya ƙare.

Daga nan ne mai Shari’a Haraja Safiyo, tayi umarnin da akai matar asibitin Ƙwaƙwalwa na Dawanau da ke jihar Kano, domin a duba lafiyar ta, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito.

People are also reading