Home Back

Tsohon Shugaban NLC, Ali Ciroma, Ya Rasu

leadership.ng 2024/5/1
Tsohon Shugaban NLC, Ali Ciroma, Ya Rasu

Tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, Ali Ciroma ya rasu.

Ciroma ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UNIMAIDTH) da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar Talata.

Wani dan uwa wanda kuma sakataren kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Borno (NUJ), Ali Ibrahim Ciroma ne ya sanar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Talata.

Sanarwar ta ce, “Ina mai bakin cikin sanar da rasuwar Kwamared Ali Ciroma, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya.

“Ya rasu ne da yammacin ranar (Talata, 2 ga Afrilu) a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

“Za a yi jana’izar mamacin a ranar Laraba da karfe 4 na yamma a gidan marigayin mai lamba 7A daura da titin Galadima kusa da asibitin Muhammadu Shuwa Memorial (Nursing Home), Maiduguri.”

Ciroma ya zama shugaban NLC ne daga 1984 zuwa 1988 har zuwa lokacin da gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Babangida ta rusa duk kungiyoyi.

Sai dai kuma a lokacin mulkin Abacha, an mayar da shi kan aikin kungiyoyi, inda aka nada shi a matsayin shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya.

People are also reading